EKITI 2018: ‘Yan sanda sun hana Fayose fita daga gidan gwamnati, bayan sun kewaye gidan

0

Yanzu haka dai ‘yan sanda 30,000 da aka girke jihar Ekiti, saboda zaben 2018 na gwamnan jihar, tuni sun fara aikin kewaye Gidan Gwamnatin jihar, inda suka hana Gwamna Ayodele Fayose fita daga cikin gidan.

Wakilai masu yawa da PREMIUM TIMES ta tura a jihar domin dauko yadda ta kaya a zaben ranar Asabar mai zuwa, sun ruwaito cewa manyan motocin ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun tare kofar shiga gidan gwamnatin, ta yadda babu wata mota mai iya shiga ko fita daga ciki.

Kwamishinan Shari’a, kuma Antoni Janar na Jihar, Kolade Kolape, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an girke jami’an ‘yan sandan tare da akalla motoci 50 tun da sanyin safiyar karfe 8 na safiyar yau Laraba.

“Tun da farko dai, gwamna Fayose ya yi niyyar ganawa da kananan ma’aikatan jihar, daga masu mataki na 1 zuwa masu mataki na 7, da misalign karfe 9 na safe.” Inji Kolade.

Kolade ya ce amma tun kafin a fara taruwa, sai ‘yan sanda suka tare kofar shiga gidan gwamnatin, suka hana kowa shiga ciki.

Ya kara da cewa an hana hatta Gwamna Fayose fita daga cikin ofishin sa, ya yin da aka rika jefa tiyagas.

Tiyagas din da aka rika jefawa ya sa tilas Fayose ya yi sauri ya koma cikin ofis

“Har yanzu din nan da na ke magana da ku, Gwamna Fayose na cikin ofis, ya kasa fita saboda barkonon tsohuwar da suka rika harbawa lokacin da ya so fita a cikin motar sa. Saboda yayin da ya zo bakin kofa a cikin mota, an tika jefa tiyagas da ya tilasta shi gaggawar komawa a cikin ofis.” Inji Kolade.

Sai dai kuma kakakin ‘yan sandar jihar, Caleb Okechukwu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda na aikin su ne na kare lafiya, rayuka da dukiyoyin jama’a kawai.

Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tambaye shi dalilin da ya sa ‘yan sanda suka datse kofar shiga gidan gwamnati, Caleb y ace su dai aikin sun a tabbatar da zaman lafiya suke yi.

Share.

game da Author