SON ta rufe manyan wuraren ajiyan kaya 21 a Kano

0

Shugaban hukumar SON Osita Aboloma ya sanar cewa hukumar su ta rufe wasu manya manyan wuraren ajiyan kaya 21 da ke dankare da jabun atamfofi a jihar Kano.

Ya sanar da haka ne ranar Talata a jihar Legas inda ya bayyana cewa hukumar ta yi haka ne saboda karya dokar hukumar da masu wadannan kaya suka yi.

” Bisa ga dokar mu kamata ya yi a sarrafa atamfa da auduga na kwarai sannan rinin da za a yi wa atamfan ba ya zuba.

” Sai gashi mun gano cewa wadannan atamfofin an hada su ne da kashi 70 bisa 100 na ruba sannan da kashi 30 bisa 100 na auduga.”

A karshe Aboloma ya ce suna da tabbacin cewa wadannan atamfofi ba a kasar nan aka sarrafa su ba, shigowa da su aka yi daga kasashen waje.

Share.

game da Author