Jami’in kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Wondi Alemu ya bayyana cewa kungiyar WHO ta fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar Kwalara a jihar Adamawa.
Alemu ya fadi haka ne a Adamawa inda ya kara da cewa za a fara yi wa mutane allurar ne ranar 10 zuwa 17 ga watan Yuli kuma a kananan hukumomin da suka fi fama da cutar.
” Binciken da muka gudanar ya nuna cewa cutar ta fara bullowa ne a ranar 12 ga watan Mayu sannan kananan hukumomin Mubi ta arewa da Mubi ta kudi ne suka fi fama da cutar.”
” A yanzu dai mutane 1,500 ne ke dauke da cutar sannan mutane 25 sun rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar.
” Tare da hadin guiwar kamfanin GAVI mun sami kason farko na magungunan alluran sannan za mu sami sauran bisa ga sakamakon da za mu samu bayan mun kammala da wadannan da muka karba.”
A karshe kwamishinan kiwon lafiya na jihar Fatima Abubakar ta bayyana cewa sun sami nasarar dakile yaduwar cutar ta hanyar wayar da kan mutane kan cutar da yadda za su iya kare kansu daga kamuwa da ita.
Ta kuma ce suna sa ran cewa wannan allurar rigakafin da aka fara zai taimaka wurin hana yaduwa da kawar da cutar daga jihar kwata-kwata.