Dan sandan da ya yi harbin dai an ce a buge ya ke da giya, a lokacin da ya harbe matar mai suna Victoria Ekpe.
Ekpe mai shekaru 32 da haihuwa, an harbe ta ne a ranar Lahadi da misalin 9 na dare a Ikot Ansa, Calabar.
Kakakin Yada Labaran ‘yan sandan jihar, Irene Ugbo, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES labarin bindige matar da dan sandan ya yi.
Ya ce tuni har an kama shi, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Wanda ake zargin ya bindige ta din, wani dan sanda ne mai suna Edu Nkanu, kuma sajen ne,
Rahotanni sun ce abin ya fara kamar da wasa, bayan da dan sandan ya koma gida, sai makwabciyar tasa ta tambaye shi me ya sayo ya zo mata da shi?
Dan sandan ya dauko bindiga ya nuna mata, y ace “kin ga abin da na zo miki da shi nan.
Ya yi wannan jawabin ne bayan da aka tambaye shi me ya sa kullum shi sai ya sha giya har ta bugar da shi?
Haka wata ganau, kudiyar wadda aka kashe din, mai suna Elizebeth Bassey ta bayyana.
Ta ce ta ji tsoro sai ta gudu cikin gida, inda daga nan ya dirka wa ‘yar uwar ta bindiga.