Rikita-rikitar da ta hana gwamnatin Buhari biyan albashin watan Yuni

0

Gwamnatin Tarayya ta sake daga ranar zaman kasafta kudaden da ta ke raba wa tarayya, jihohi da kananan hukumomi a karo na biyu.

Taron da aka gudanar a jiya Talata bai harfar da da’ mai ido ba, yadda tilas aka taron zuwa ranar Alhamis mai zuwa domin kammala tattaunawar a samu a biya ma’aikata albashin su na Yuni.

Wannan ne karo na biyu da aka daga taron. Abin kuma ya kawo tsaikon biyan albashi ga ma’aikatan tarayyaya, jihohi da kananan hukumomin gwamnati.

Wani jami’in gwamnatin tarayya ya shaida wa manema labarai cewa an sake yin ja-in-ja a wurin kasafta kudaden da ake bai wa tarayya da jihohi, don haka an daga zaman sai ranar Alhamis zai zuwa.

Tsaikon da aka samu ya biyo bayan rashin samun kudaden shiga daga ribar man fetur da kamfanin mai ‘NNPC’ ke tara wa gwamnati.

Ganin babu wadatattun kudade ne ya sa tilas aka daga taron a makon da ya gabata.

Mambobin da ke taruwa domin su kasafta kudaden, sun hada da kwamishinonin jihohin kasar nan da kuma akantoci na kowace jiha.

Dukkan su sun zargi NNPC da kasa tattara kudaden shiga na ribar mai, a watan da ya gabata domin kasaftawa.

Kakakin Hukumar NNPC, Oganmadu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa NNPC ta ware wa gwmanoni Naira bilyan 147 da hukumar ta yi yarjejeniya za ta rika bayarwa a duk wata.

Tuni dai ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi sun fara guna-gunin rashin biyan su albashin watan Yuni da har yau ba a yi ba.

“Jama’a yau fa watan Yuni kwanan sa 40 cif, amma har yau albashi shiru ka ke ji!” Haka wani Farfesa da ke koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano ya rubuta a shafin sa, a jiya ranar da watan Yuli ya kwana goma.

Share.

game da Author