Ribadu ya nemi a kara gudanar da ayyukan harkokin fetur a sarari

0

Shugaban Hukumar EFCC na farko, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa duk da an samu ci gaban rage kumbiya-kumbiya da harkalla a fannin man fetur a kasar nan, duk da haka akwai bukatar kara kaimi wajen ganin ana fayyace hada-hadar fannin a fili.

Da ya ke gabatar da lacca yayin kaddamar da mujallar The BalueChain, a jiya Talata a Abuja, Ribadu ya kara da cewa gudanarc da kowace harka kan ka’ida kuma a sarari na da muhimmanci har ma ga fannin inganta tattalin arzikin masana’antu.

“Rika fayyacewa da fito da ayyuka a sarari kan ka’ida a fannin harkokin mai, abu ne da ya wajaba. Yin ayyuka keke-da-keke na da matukar muhimmanci, saboda hakan na kara jaddada tattalin albarkatun kasa tun daga hako su har kaiwa ga yin amfani da su.”

Ribadu shi ne Shugaban Kwamitin Sa-ido da Bincike kan Kudaden Ribar Man Fetur a cikin 2012.

Ya yarda da cewa shekarun da aka shafe ana bushasha da almubazzanci da kudaden man fetur sun sa da dama guyawun su duk sun sare, har ta kai ana yi wa Najeriya zolayar cewa, “mai dimbin fetur din da ba shi da albarka.”

Ribadu har yau ya koka da yadda a shekarun baya Najeriya ta rika asarar ribar kudaden man fetur ta hanyar rashawa wajen aikin hako man fetur da kuma yadda aka rika yin kumbiya-kumbiyar bada lasisi a kamfanin.

Sai da kuma yace Najeriya a yanzu ta yi kokari wajen kokarin hana harkalla, kuma ta na ta na hana cin rashawa ta hanyar amfani da jami’an tsaro.

Share.

game da Author