A dalilin rashin fahimta da neman karyata satifiket din karya da minista Kemi tayi wa mutanen Najeriya, PREMIUM TIMES ta nema irin wadannan satifiket na wadanda suka kammala aikin bautar kasar su a shekarar 2009 da kuma wadanda aka dauke wa nauyin yin bautar kasar a wannan shekara ta 2009.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta gano cewa Kemi ta mallaki satifiket din shaidar yin bautar kasa ne na jabu, shekaru da yawa bayan da ta kammala jami’a.
Dokar Najeriya ta tanaji hukunci ga wanda duk ya ki zuwa aikin bautar kasa da gangan matsawar dai bai cika shekaru 30 ba.
Takardun karatun Kemi da ke hannun PREMIUM TIMES sun nuna cewa hukumar ta ba ta satifiket na yafe mata zuwa bautar kasa a shekarar 2009, a bisa yawan shekaru.
Ga su:

