Shugaban Karamar Hukumar Dutse ta Jihar Jigawa, ya zargi abokin hamayyar siyasar sa da ingiza wasu ‘yan mazabar sa har suka yi masa dukan tsiya.
Hasalallun dai sun yi wa Alhaji ‘Yargaba kofar-raggo ne, daga nan suka yi masa taron-dangin da suka rika jibgar sa, a bisa zargin ya karkatar da kudin da gwamnatin jihar ta dawo da shi, watau raba kudi ga mazabun jihar a kowane wata.
Dama PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin zargin da jama’ar ke wa Yargaba da yin harkallar raba kudaden ga wadanda ba su cancanta ba.
Da dama kuma sun yi zargin cewa ya danne kudaden ne bai raba ba, har suka gargade shi da ya fito da kudaden ya raba wa kowa hakkin sa.
An tare Shugaban Karamar Hukumar ne a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta fita. Nan take suka nemi ba’asin kudin na su.
Yargaba ya shaida musu cewa shi bai ma san ko an biya kudaden ba. Jin wannan furuci daga bakin sa, sai suka fusata, suka hau shi da jibga.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da sai da aka kekketa rigar Shugaban Karamar Hukumar, har sai da ta kai mafusatan suka rika yin watandar kyallayen rigar, wannan ya keta ya ba wancan shi ma ya keci rabon sa.
Nan da nan su ka kewaye Sakateriyar Karamar Hukumar, suka hana shi fiicewa.
Yargaba dai ya yi ta-maza, ya kubuce ya afka cikin sakateriya, sai dai duk da haka sai da mafusatan suka yi mata zobe.
Daga bisani dai jami’an tsaro sun kai dauki a makare, suka fasa taron. Wasu sojojin da ke sintiri sun kai dauki domin su kwantar da rikicin. Sai dai sun samu mafusatan na ta rera wakokin aibata shugaban karamar hukumar.
Kakakin ‘Yan sandan Jigawa, Abdul Jinjiri ya ki cewa komai, a bisa dalilin cewa bai kai ga samun rahoton jibgar da aka yi wa Yargaba ba.
Daga baya Yargaba ya musanta cewa ya ci kudin ko ya maye gurbin sunayen wasu mutane da na kusa da shi.
Ya ce Hon. Sule ne ya birkita sunayen bayan da aka aika da wadancan sunaye na ainihi daga Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.
Sai dai kuma Dan majalisar Dokoki Sule, ya ce karya Yargaba ke yi masa da sharri, ya ce babu yadda za a yi ya kawo cikas ga dokar da su ne ma suka kafa ta kuma suka amince da aiwatar da komai dangane da raba kudaden.
“Ina ruwana da sunaye. Shugaban Karamar Hukumar ne fa da kan sa ya yi sanarwa a radiyo cewa ranar Litinin duk a je a karbi kudaden. Abin takaici gare shi, sai taron ya karke da rikicin da ya ci dukan tsiya.”