Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sake sabunta dokar hana hawa da babura a kananan hukumomi 14 dake jihar.
Kakakin rundunar Muhammad Shehu ya sanar da haka ranar Litini a Gusau.
Shehu ya bayyana cewa dokar ta hana a yi amfani da babura a jihar daga karfe shida na yamma zuwa bakwai na safe sannan za a fara aiki da dokar ne ranar Talata 10 ga watan Yuli.
‘‘Mun sabunta wannan doka ne domin kawar da rashin zaman lafiya da ake fama da shi a jihar.Saboda haka muke kira ga mutane da su yi biyayya ga wannan doka domin samun zaman lafiya mai dorewa a Jihar.
A karshe Shehu ya yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da hada hannu da jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya na din-din-din a fadin jihar.
Discussion about this post