Dalilai 10 da ya sa ma’aikatan gidan radiyo Najeriya FRCN suka yi zanga-zanga

0

A ranar litinin ne ma’aikatan gidan radiyon tarayya da babban birnin tarayya Abuja FRCN da babban tashan ta dake Kaduna suka fito zanga-zanga cikin bakaken kaya suna kira ga gwamnati da ta waiwaye su kan halin da suke ciki.

Kamar yadda wadanda suka tattauna da wakilan mu a hedikwatar ma’aikatar wato Radio House dake Abuja sun shaida mana cewa

1 – Rashin ruwa kawai ya addabi ma’aikatan gidan radiyo.

2 – Babu wutan lantarki

3 – Takardun rubutu ma bamu da shi ballantana alkalumma.

4 – Ba a biya mu kudaden tafiye-tafiye na aiki ba tun daga shekarar 2010.

5 – Ba a biya mana kudaden fansho

6 – Bamu da kujerun zama a ofisoshin mu sai dai kayi ta makalewa sannan ma’aikata ba su da kananan radiyo na daukar Labarai.

7 – Da kudin mu muke balaguron aiki sannan babu albashin kirki.

8 – Sannan ko mun yi tirenin a makarantar karo ilimin aikin radiyo dake Legas, ba ya yi mana amfani domin ba za ka samu karin girma da shi ba.

9 – Ba a biyan mu kudin gida

10 – Ba a biyan mu kudin abinci

Sai dai kuma shugaban gidan radiyon na kasa, Mansur Liman ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi musu alkawari share musu hawaye nan ba da dewa ba.

Share.

game da Author