Suwaiba ta roki kotu ta tilasta wa tsohon mijinta ya biya ta kudin gadon ta da ya cin ye a Kaduna

0

A yau Litini ne wata mata mai suna Suwaiba Suleiman ta kai karan mijinta mai suna Harisu Abubakar a kotun shari’a dake Kaduna don kin biyan ta rancen kudin gadonta da ta siyar ta bashi.

Suwaiba ta bayyana wa kotu cewa a kwanakin baya Harisu ya lallabeta da ta siyar da gadonta ta ranta mishi wannan kudin gadon.

” Bayan ya gama kashe kudin tas, sai ya bini da saki kuma. Sannan bayan haka mahaifina na bin shi bashin naira 13,000

” Ina rokon kotu da ta tilasta wa Harisu ya biya ni kudin gadona ko kuma ya yi mini sabuwar gado a makwafin kudin sannan ya biya bashin da mahaifina ke bin shi.”

Shi kuwa Harisu bai musanta bashin Naira 13,000 da mahaifin Suwaiba ke bin sa ba amma yace Suwaiba ce da kanta ta siyar da gadonta sannan ta bashi wannan kudin gado batare da ya lallabeta ta yi haka ba ko kuma ya zuga ta.

A karshe Harisu ya amince ya biya Suwaiba kudin gadonta Naira 10,000 tare da bashin Naira 13,000 da mahaifinta ke bin shi.

Sannan alkalin kotun Dahiru Abubakar ya yanke hukuncin cewa duk wata Harisu zai dunga biyan Suwaiba Naira 5,000 domin kula da dan da suka haifa tare.

Share.

game da Author