Mutane 1,564 sun kamu da cutar Kwalara a jihar Adamawa

0

Jami’i a hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar Adamawa Amos Ujulu ya bayyana cewa a shekarar 2018 mutane 1,564 sun kamu da cutar kwalara sannan mutane 26 sun rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar a jihar.

Ya fadi haka ne a zaman da kwamitin zantarwa na jihar ta yi a makon da ya gabata a Yola.

” Kananan hukumomin da wadannan kauyukan suka yi fama da cutar sun hada da Maiha,Mubi da Mubi ta kudu sannan cutar ta yadu zuwa wasu bangarorin kasar Kamaru.”

Ujulu yace jihar za ta bukaci Naira miliyan 22 domin kawo karshen yaduwar cutar a jihar.

Share.

game da Author