RIKICIN APC: Muna bayan Saraki – Inji APCn Kwara

0

Jam’iyyar APC reshen jihar Kwara, ta bayyana cewa ita biyayyar ta kacokan a kan Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ta ke.

Daga nan sai ta sake fitowa baro-baro ta ce ta tabbata tuni aka sa takobi aka fille kan jam’iyyar, ta yadda babu sauran hadin kai, an gurgunta jam’iyyar, kuma yi wa fuskar ta dameji, tun ma kafin a fille mata kan hadin-kai.

Jam’iyyar ta fitar da wannan sanarwa ce bayan da Kotin Koli ta wanke Saraki daga zargin kin bayyana takamaimen kadarorin sa.

An dai shafe sama da kwanaki dubu daya ana tafka shari’ar Saraki, inda daga bisani bayan ya daukaka kara a Kotun Koli, ya yi nasara.

“Mu na cikin matukar murna da farin cikin ganin yadda Kotun Koli ta wanke Sanata Saraki, kuma dama mun san bai aikata laifin komai ba. Kawai dai wani tuggu ne aka kitsa masa.

Daga nan sai jam’iyyar ta dora laifin tuggun da aka yi wa Saraki, a kan wasu ‘yan dandatsar siyasa da suka yi amfani da hukumar ICPC domin cimma wata bukata ta su.”

“Mu ba butulu ba ne, komai ruwa komai iska mu na tare da Sanata Saraki.”

Share.

game da Author