Za a yi wa yara 808,470 allurar rigakafin cutar shan inna a jihar Cross River

0

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Cross Rivers Betta Edu ya bayyana cewa gwamnati na shirin yi wa yara 808,470 allurar rigakafin cutar shan inna a jihar.

Ya kuma kara da cewa ko da yake wannan allurar itace karo na biyu gwamnati ta dauki ma’aikata 7,588 da za su yi wa yara allurar na tsawon kwanaki hudu.

” Mun dauki ma’aikata 7,588 wanda za su yi wa yara allurar rigakafin cutar a kananan hukumomi 18 a jihar na tsawon kwanaki hudu.”

Share.

game da Author