Harkallar shaidar NYSCn Kemi ya harzuka ‘yan Najeriya

0

‘Yan Najeriya sun harzuka sosai bayan fallasa harkallar da Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta yi, inda ya tabbatar da cewa kiri-kiri ta ki zuwa aikin bautarc kasa wato NYSC, a lokacin da ta kammala babbar kwalejin ta.

PREMIUM TIMES ta fallasa yadda Kemi ta rika gabatar da satifiket din dauke mata aikin bautar kasa na bogi, bayan da ta kammala karatu a Babbar Kwalejin Fasaha ta East London, a cikin 1989.

Akasarin wadanda suka tofa albarkacin bakin su, sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa kwamitin bincike domin a tabbatar da gaskiya ko akasin gaskiyar wannan labara da PREMIUM TIMES ce ta bankado shi.

Mafi yawan wadanda suka yi rubuce-rubuce a soshiyal midiya, sun cika da mamakin yadda hukumomi da jami’an tsaron bincikenn kwakwaf suka kasa gano wannan bahallatsa ta Kemi, har sai da PREMIUM TIMES suka fallasa ta.

Wasu kuma sun nuna takaicin yadda wata wadda kiri-kiri ta ki zuwa aikin bautar kasa, amma an ba ta babban matsayi a kasa, alhalin ga wadanda suka je dautar kasar nan zube a kasar nan ba tare da samun aikin komai ba.

Har ila yau, wannan labari da PREMIUM TIMES ta buga, ya haifar da sabuwar sara da gasa a soshiyal midiya, inda wasu suka rika daukar hoton katin shaidar yin aikin bautar su kasa suna turawa a shafukan su a Facebook.

“Da yawa sun rika rubuce-rubucen cewa a kore ta kawai, tunda dai ta yi harkallar takardar NYSC. Wasu sun rika cewa an kawo kan wata babbar gabar da za a kara auna gwamnatin Buhari domin a gani shin zai gaggauta korar ta idan har an same ta da rashin gaskiya, ko kuwa a wannan ma dakewa zai yi kamar yadda ya dake aka manta da batun Babachir Lawal da kuma Abdulrashid Maina?

Dayo Williams ya bayyana a shafin san a Faceboook cewa, “Ina sauraren na ji ko naga Ministar Kudade Kemi Adeosun ta kira taron manema labarai domin ta bayyana na ta ba’asin, kowa ya ji.

Haka su ma masu rajin kare hakkin jama’a da dimokradiyya irin su Olarenwahu Suraju sun sun koka da lamarin.

Da yawa na cewa ta fito ta kare kanta, a gaggauta bincken ta kuma a yi waje rod da ita.

Dimbin masu kallon abin ta fuskar majalisar tarayya kuma, sun nuna takaicin yadda Majalisar Dattawa ta rika tatsar biliyoyin kudade a wurin Kemi.

Share.

game da Author