Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa hadin kan kasar nan ba abin yin wasa ko yi masa rikon-sakainar-kashi ba ne, balle har wani ya shigo da son ran sa ya nemi sai an yi masa abin da ya ke so idan ana so a ci gaba da tafiya tare.
Daga nan sai ya ja hankalin kafafen yada labarai su guji yada abubbuwan da ka iya haddasa mummunan rikici a kasar nan.
Obasanjo ya yi wannan bayani a ranar Asabar yayin da ya zama mai masaukin baki a bikin shekara na Hukumar Gudanarwar Editocin Tsare-tsaren kamfanin Penpushing Media.
An gudanar da taron a Babban Dakin Taro na Laburaren Obasanjo da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Ya ce sai ‘yan Najeriya sun riki kowane bangare na kasar nan a matsayin abokan gudu tare da tsira tare, sannan kasar nan za ta iya ci gaban da za a yi tinkaho da ita.
Ya ce bambancin kabilu da yaruka da addini wata albarka ce ga kasar nan, ba matsala ba ce.
Daga nan sai ya nuna takaicin sa matuka gaya a kan yadda jama’a da dama suka fara dawowa daga rakiyar gaskata kafafen yada labarai sosai.
Daga cikin manyan bakin da suka shugabanci zaman tattaunawar har mawallafin PREMIUM TIMES, Dapo Olorumi.