Tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, Olisa Agbakoba, ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi a kasar nan “ya zama wajibi” domin ta haka za a gaggauta magance matsalar tsaro a cikin jihohin nan.
Agbakoba ya yi wannan jawabin a lokacin da ya ke ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, a yau Litinin a Lagos.
Fitaccen lauyan ya na magana ne a kan yawaitar kiraye-kiraye kan bukatar kafa ‘yan sandan jihohi ganin yadda matsalar tsaro ke kara muni a yawancin jihohin kasar nan.
Tuni dai Majalisar Dattawa ta umarci kwamitin duba kundin tsarin mulki da ya sake nazarin doka, domin a duba yi mata kwaskwarimar yadda za ta bada damar kafa ‘yan sandan jihohi a fadin kasar nan.
Agbakoba ya ce ‘yan sandan tarayya ba su iya wadatar da tsaro a fadin kasar nan, don haka ‘yan sandan jiha na da muhimmancin rawar da za su rika takawa a jihohi baki daya.
A duniya nan Najeriya ke kadai mu ke da irin wannan tsari, inda Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda zai kwanciyar sa a Abuja, amma ya ce wai daga can ya ke kallon duk abin da ke gudanar a Najeriya baki daya.”
Idan za a iya tunawa, kwanan baya an yi korafi dangane da karancin ‘yan sandan da za su rika gudanar da tsaro a kasar nan.
Wani bincike ya fallasa cewa da yawan ‘yan sandan Najeriya duk gadi suke yi a hannun ko ga gidajen wasu manyan kasar nan.”