ICPC ta fara binciken Jami’an gwamnatin da suka karkatar da guraben karo ilimi na CCCEC ga ‘ya’yan su

0

Hukumar Ladaftar da Ma’ailkatan Gwamnati (ICPC), ta fara binciken Ministoci da manyan jami’an gwamnatin Muhammadu Buhari, wadanda suka danne guraben karo ilimin da kamfanin CCCEC ya ware wa ‘ya’yan talakawan Najeriya zuwa China.

PREMIUM TIMES ce ta gudanar da wani gagarimin binciken da ta bankado yadda aka yi abin da Hausawa ke cewa ‘girma ya fadi, rakumi ya shanye ruwan kasko, ya hana kaji da ‘ya’yan ta’.

Kafanin gina titin jiragen kasa (CCECC) ya ware wa daliban jami’a guraben karo ilimi zuwa China, amma ministoci da manyan jami’an gwamnati suka rabe guraben ga ‘ya’yan su, ‘ya’yan dangi da na dangin matan su.

Makonni biyu da suka gabata, PREMIUMN TIMES ta fallasa sunayen ministocin da aka raba wa guraben, ciki har da gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar.

Har yau babu wanda ya fiton ya karyata labarin wanda wannan jarida ta fallasa.

Wannan wala-wala dai ta harzuka dimbin matasan kasar nan, inda cikin mako biyu da suka gabata, suka yi dafifi a harabar Ma’aikatar Harkokin Sufurin Kasar nan a Abuja, har suka rufe babban titin da ya hada Babban Masallacin Juma’a da Central Area.

An hana ‘ya’yan talakawa zuwa yin intabiyu domin tantancewa, wanda hakan ya kara fallasa harkallar bayan PREMIUM TIMES ta fallasa labarin kuma ta buga wasikun da aka rika aika wa ministocin a boye cewa kowa ya kawo sunayen yaran da ya ke so a tura a asirce.

Dimbin ‘yan Najeriya sun kidima da wannan labarI, inda a take suka nemi a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa, a gano yadda wadanda aka dora wa amanar al’umma suka kware wa talakawa baya, alhali su ne aka rika bi kusfa-kusfa ana neman kuri’un su.

AN FARA BINCIKE

Majiya mai tushe ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ICPC ta fara bincike gadan-gadan, kuma tuni tun ranar Alhamis, 5 Ga Yuli, 2018, ta gayyaci kamfanin CCECC, inda kamfanin ya tura wakilan sa domin su maida bayani.

An kuma gayyaci Sabi’u Zakari, wanda shi ne Babban Sakatare na Ma’aikatar Harkokin Sufuri, kuma shi ne ya rika aika wa Ministoci da manyan jami’an gwamnati wasikar cewa su turo sunaye a asirce.

Share.

game da Author