Tabbatattu kuma sahihan shaidun bayanai rubutattu sun tabbatar da cewa Ministar Harkokin Kudi, Kemi Adeosun ba ta yi aikin bautar kasa ba, kuma a lokacin shekarun ta ba su kai na wadda aka dauke wa aikin bautar kasar ba.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Kemi ta mallaki takardar shaidar yin bautar kasa ne na jabu, shekaru da yawa bayan da ta kammala jami’a.
Dokar Najeriya ta tanaji hukunci ga wanda duk ya ki zuwa aikin bautar kasa da gangan matsawar dai bai cika shekaru 30 ba.
Akwai daurin shekara uku ko tarar naira dubu biyu, ga wanda ya karya wannan doka, kamar yadda Kemi ta yi.
Akwai kuma daurin shekara uku da doka ta tanadar ga wanda ya kuskura ya buga satifiket na karyar yin bautar kasa.
Takardun karatun Kemi da ke hannun PREMIUM TIMES sun nuna cewa hukumar ta ba ta satifiket na yafe mata zuwa bautar kasa a shekarar 2009, a bisa yawan shekaru.
YA AKA YI HAKA?
Adeosun dai ta kammala babbar kwalejin fasaha, wato London Polytechnic cikin 1989 ta na da shekaru 22.
Bayanan haihuwa sun nuna cewa an haife ta cikin 1967.
Wannan kwaleji ta canja suna zuwa Jami’ar Gabashin Landan cikin 1992.
To ita kuma Adeosun ta karbi satifiket na dauke mata nauyin zuwa bautar kasa bayan da aka canja wa makarantar suna ne.
Tunda ta kammala makarantar a lokacin da ta ke shekaru 22, ya zama tilasa ne ta yi aikin bautar kasa na shekara daya a Najeriya idan har ta na so a dauke ta ko ma wane irin aiki ne a kasar nan.
Sai dai kuma bayan ta kammala, sai ta yi zaman ta a London, ta ki dawowa Najeriya ta yi bautar kasa.
A wancan lokacin cikakken sunan ta shi ne Folakemi Oguntomoju, kafin ta gutsire tsawon sunan na ta zuwa Kemi.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Kemi ta yi aiki a wurare da dama a kasar Ingila bayan da ta kammala karatu a can cikin 1989.
BAYA BA ZANI
Satifiket na afuwar zuwa aikin bautar kasa mallakar Minista Kemi, ya nuna cewa Darakta Janar na lokacin, Yusuf Bomai ne ya sa masa hannu a ranar 9 Ga Satumba, 2009.
Sai dai kuma binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta gudanar, ya tabbatar da cewa wa’adin Bomai ya kare tun cikin watan Janairu, 2009.
HARAMTATTUN AYYUKAN DA TA YI
Kemi ta yi amfani da satifiket na karya, ta yi aiki a ‘Quo Vadis Partnerships a matsayin manajar darakta, ta yi kwamishinar kudi a jihar Ogun, kuma yanzu ta na Ministar Kudi ta tarayya.
Akwai dokokin kasa na 1973-1974 da suka gindaya cewa sai mai neman aiki ya cika wadansu sharudda kafin a dauke shi aiki. Amma Kemi ta yi aiki wurare uku a Najeriya ba tare da cika wadannan sharudda ba.
Cikin 2011 ne Gwamna Ibikunle Amosun ya dauke ta ta zama kwamishinar kudi ta jihar Ogun.
Cikin Nuwamba, 2015 Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta Ministar Kudi, amma a haka ta samu tsallakewa bayan da ta mika wa SSS da Majalisar Dattawa satifiket na karya
YADDA AKA GANO
PREMIUM TIMES ta shafe watanni ta na neman gano sahihancin satifiket din.
Kwakkwaran bincike a hedikwatar NYSC ta tabbatar da cewa na bogi ne irin wanda ake bugawa a kasuwa, ka na tsaye, a buga maka ka biya ka kama gaban ka.
Ma’aikatan hukumar da dama sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa da ganin satifeket din an san na karya ne ba sahihi ba ne.
PREMIUM TIMES ta yi ta rokon neman ba’asi daga hukumar har tsawon lokaci, amma ba ta yi magana dangane da batun ba.
SHIYA SA MAJALISAR DATTAWA KE TATSAR KUDI A HANNUN TA
PREMIUM TIMES ta gano cewa Majalisar ta gane Kemi na da fojaren satifiket, shi ya sa suke ta tatsar ta makudan bilyoyin kudade, ko da kuma Shugaba Muhammadu Buahri bai amince a bayar da kudaden ba, to ita sai ta kamfata ta ba su.
Ita ma Ma’aikatar Harkokin Kudade ta ki cewa komai a kan batun.
Discussion about this post