Kasar Brazil da ake wa zaton ita ce zata lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya yau dai ta ci taliyar ta karshe.
Kasar Belgium ta doke Brazil da ci 2-1 a wasa na biyu da aka buga ranar Juma’a.
Tun da farko dai kasar Belgium ne ta zura wa Brazil kwallaye 2 a raga inda a cikin mintuna 10 da kammala wasan Brazil ta samu damar jefa kwallo daya.
Yanzu dai shima Neymar da ya rage a gasar cikin mashahuran ‘yan wasan da suka zo kasar Rasha zai tattara nashi-ina-nashi ya koma gida kamar yadda su Messi da Ronaldo suka yi.
A wasan farko da aka buga da yammacin Juma’a, kasar Faransa ta doke Urugay da ci biyu babu ko daya.
Anan ma fitaccen dan wasan Barcelona, Suares ya kasa ceto kasar tasa don ta iya kaiwa zagayen na kusa da karshe.