Rashin sanin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau na kawo mana cikas – Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin sanin adadin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau a kasar nan na cikin kalubalan dake hana Najeriya samun tallafin magungunan cutar daga kasashen waje.

Shugaba Buhari a fadi hake a fadar gwamnati a yayin kaddamar da taron fara kididdiga na yawan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a kasar.

Buhari ya ce domin kawar da irin wadannan matsalolin ne gwamnati ta amince kan yin kidaya domin samun adadin yawan mutanen dake dauke da cutar.

“Sanin adadin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau zai taimaka mana wurin samun isassun magungunan kawar da cutar”.

Buhari ya ce kidayan zai dauki tsawon watanni shida a duka fadin kasar nan.

Share.

game da Author