Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya cikin irin maganganun da yakan ya masu kama da habaici, mai hankali ke ganewa a shafin sa ta tiwita ya ce ” Mu dinnan fa da ake muzgunawa, aka maida saniyar ware muna hanyar mu ta ficewa wannan kazamar gari kan dawakan mu, rakuman mu dauke da kayan mu a hanyar mu ta ficewa Misra garin azzalumin Sarki, Fir’auna. Yanzu muna bakin tekun baharmaliya, za mu fice wannan kazamiyar kasa, kasar zalunci da kamakarya.”
Masu yin fashin baki a harkar zantuka, dabo da habaici sun danganta wannan furuci na sanata Shehu Sani da irin abubuwan dake faru a siyasar Najeriya musamman kamayamayar da ta damalmale jam’iyyar APC da tun a jiya Laraba, aka fara samun ballewar wasu ‘yan Jam’iyyar masu suna jam’iyyar APC ta hakiki, wato ‘Reformed APC.”
Sanata Shehu Sani ya dade yana yi wa jam’iyyar APC hannun ka mai sanda, sannan yakan fito karara ya nuna mata kuskuren ta sannan ya roki jam’iyyar ta gyara. Ba jam’iyyar APC din ba kawai hatta shugaban kasa Muhammadu Buhari ma bai bari ba wajen tunatar da shi idan aka yi kuskure.
Shehu Sani na daga cikin Sanatocin da ake tunkaho da su a majalisar dattawa, ganin irin gudunmuwar da ya kan bada wajen tofa alabarkacin bakin sa don ganin an sami ci gaba a kudurorin da zasu ciyar da kasa gaba.
Wani babban abin da yayi wa kasa Najeriya da za a dade ba a manta dashi ba shine yadda yayi ruwa yayi tsaki aka kori sakataren gwamnatin tarayya Lawal Babachir bayan kwamitin sa ta kama shi dumu-dumu da hannu a waskewa da kudin kwangilar cire ciyawa a rafin Yobe.
Duk da dan jam’iyyar APC ne, bai biye wa son rai ba, ya tsaya kai tsaye wajen ganin an bi wa talakawa hakkin su da hakan ya sa dole Buhari ya kore Babachir ba wai don yana so ba domin kuwa sai da aka yi ta kai ruwa rana tukunna.
Idan ba a manta ba a kwankin baya ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tsitsine musu Albarka, dukkan su su uku sanatocin dake wakiltar Kaduna a majalisar dattawa, Wato sanata Shehu Sani, Sanata Sule Hunkuyi da Sanata Danjuma Lar saboda sun ki saka masa hannu ya ciyo bashi daga bankin duniya.
Hakan dai daya ne daga cikin yakin basasar da ake ta gwabza wa tsakanin gwamna El-Rufai da sanata Shehu Sani.
Zaman lafiya tsakanin su ya dada tabarbarewa ne tun bayan rashin jituwa da suka sami watanni kadan bayan an kafa gwamnati a 2015.
Irin wannan rashin jituwa ya shafi kusan duk jihohin da APC ke mulki ne.
A Abuja kuwa, da’ga ce aka ja tsakanin majalisar Tarayya duk su biyun da shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Duk wanda ya san yadda a ka gudanar da mulki a gwamnatocin baya, zai san lallai an samu baraka matuka a wannan gwamnati musamman irin zama doya da manja da ake yi tsakanin majalisa da bangaren zartaswa.
Tun da farko dai ita kan ta uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta koka kan yadda maigidanta ya ke jan ragamar mulkin kasar inda har tayi barazanar kin mara masa baya idan har yaci gaba akan wannan tafarkin da ya dauka. Haka shi kan sa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da ake ganin dan lelen shugaba Buhari ne ya taba fitowa ya soke gwamnatin musamman yadda take tafiya da kuma bata shawarwari.
Yanzu dai ‘yan Najeriya sun gwalo idanuwar su kuru-kuru suna jiran suga yadda abubuwa zasu wakana daga yanzu har zuwa lokacin Zabe.
Discussion about this post