Alkali ya hana Metuh mai laifin miliyan 400 fita neman magani, ya bar Badeh mai laifin biliyan 4 fita waje ziyara

0

Hausawa sun dade suna cewa shari’a sabanin hankali. Hakan kuwa ta tabbata yau a Abuja, bayan da Mai Shari’a Akon Abang na Babbar Kotun Tarayya ya amince wa Tsohon Hafsan Tsaron kasar nan, Alex Badeh ya fita kasar waje zuwa ziyarar iyalan sa amma Olisa Metuh dake neman a barshi ya je asibiti ya gagara.

Ana neman zunzurutun naira biliyan 3.97 daga hannun Alex Badeh.

Wannan hukunci da Okon ya yanke ya jefa wasu manyan lauyoyin kasar nan cikin waswasi, damuwa da jefa alamomin tambaya.

Mai Shari’a Okon din nan ne ya jajirce ya hana tsohon kakakin yada labaran PDP, Olisa Metuh fita waje domin maganin rashin lafiyar da ke damun sa.

Ana tukumar Metuh da wawurar naira bilyan 400.

Tuhumar da ake yi wa Badeh ta yi muni matuka, kuma ta fi illa bisa ga wadda ake tuhumar Metuh.

Alex Badeh ya wawuri kudin da ake zargin ya kwashe a lokacin ya na ma’aikacin gwamnati.

Shi kuma Metuh, dan siyasa ne, ba ma’aikacin gwamnati ba ne.

Kudin da ake zargin suna hannun Metuh, kashi 10 ne kacal bisa 100 na yawan kudaden da ake nema a hannun Alex Bade.

Yayin da ake tuhumar Olisa Metuh da aikata laifuka bakwai, ana tuhumar Badeh da aikata laifuka 14, kuma duk a kotu daya, karkashin mai shari’a daya amma Alkali Okon ya fi ganin Badeh ya je yawon ganin Iyalan sa da ke zama can a kasar waje ya fi ya amince wa wannan da yake ta suma a kotu, yanan neman a barshi ya tafi neman magani kasar waje.

Share.

game da Author