Jami’ in asusun Kula da kanana yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Sanjana Bhardwaj ya bayyana cewa kashi 55 bisa 100 na jarirai 1000 da ake haihuwa a jihar Kebbi na mutuwa a duk wata.
Ya ce sun gano haka ne bayan gudanar da binciken da suka yi a Najeriya tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017.
Bhardwaj ya ce mutuwar wadannan jarirai a jihar Kebbi na da nasaba lalacewar kiwon lafiya da matsalolin da ake samu a jihar.
Ya ce wadannan matsaloli sun hada da cutar sanyi dake kama hakarkari, cututtukan dake kama kafofin shakar iska na jariri da ke cushe masa hanyoyin yin numfashin sa da sauran su.