Ina rokon ku da kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan r-APC

0

Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya roki hasalallun ‘yan jam’iyyar APC da suka kirkiro sabuwar APC mai suna ‘APC ta hakika’ APC wato ‘refined APC’ da su mai da wukan su su dan bashi lokaci domin shawo kan matsalolin da ke cunkushe a jam’iyyar.

“Ina rokon ku da kuyi hakuri.” Inji Oshiomhole

Ya ce yana so ya tabbatar musu cewa tabbas za su iya tafka kuskure amma a matsayin sa na sabon shugaban jam’iyyar yanzu, idan aka tunashe shi zai waiwayo ya gyara wadannan kurakurai.

Ya kara da cewa yanzu ne aka zabe su kuma da shi da sauran sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar za su mai da hankali wajen ganin sun gyara kurakuran aka yi a baya.

” Ni dinnan zan yi aiki da duk wani dan jam’iyyar mu sannan kuma zan hado kan kowa kuma za ayi tafiya ne tare babu wariya ko kumu nuna bambamci ga wasu. Ina bukatan ku dan bani lokaci domin ni zan bi diddigin yadda komai yake ne tun a farko in kuma gyara.” Inji Oshiomhole

Cikin korafe-korafen da sabuwar APC din tayi sun hada da zaben su Oshiomhole da akayi a maoknnin da suka wuce, cewa ba a bi ka’ida ba sannan da yawa daga cikin wakilan jam’iyyar ba a bar su sun yi zabe ba.

A nashi tsokacin, kakakin jam’iyyar Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa jam’iyyar za ta koma ta duba wadannan korafe-korafe domin a gyara su.

Share.

game da Author