Malamai na cinye wa ‘yan makaranta abinci a Jihar Kaduna

0

A bincike da wa wata kungiya mai suna COGEN dake aikin bin makarantu domin duba yadda ake ciyar da ‘yan makaranta a makarantun gwamnati, sun gano cewa a jihar Kaduna malamai ne ke lunkume abincin yara maimakon su basu.

Shi dai wannan abinci gwamnatin tarayya ce take ciyar da daliban makarantun gwamnati dake fadin kasar nan.

A binciken da COGEN tayi, ta sake ganowa cewa wasu ‘yan siyasa na karbar kudade daga hannun masu dafa abinci da sunan wai su ba ‘yan jam’iyyar APC bane, ko su bada ko a canza su da hakan yasa wasu ‘yan jam’iyyar PDP suka hana ‘ya’ayn su cin abinci kwata-kwata a jihar. Cewar wani Monday John.

Esther Gushe, wanda mataimakiyar shugaban makarantar Firamare na Aduwan III ta tabbatar da wadannan sakamakon binciken inda ta kara da cewa lallai suna samun karancin abincin da ake kawo wa daliban.

Yakubu Kyari, da jami’i ne mai kula da wannan shiri ya ce sukan bukaci akalla kiret din kwai 700 duk mako amma da kyar ake kawo musu kiret 300 zuwa 400, da hakan kan sa su sami ya mutsin gaske da kuma rashin isa.

Shugaban kungiyar COGEN Ebenezer Omolekun, ya bayyana cewa a wasu makarantun ma mutum 4 suke raba kwai daya sannan biskit ma mutane 2 zuwa hudu ke rabawa.

Bayan haka kuma yace sun bi makarantu 420 ne dake fadin jihar domin duba yadda yanayin bada abincin yake awuraren.

Share.

game da Author