Idan dai ba wani canjin shawara aka samu ba, a yau dinnan ne wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da ya hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, shugaban Majalisar Wakilai da tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso za su kafa sabuwar kungiya mai suna sabuwar APC, nAPC.
Sakataren kungiyar kuma tsohon jigo a jam’iyyar Muhammadu Buhari na CPC a wancan lokaci, Buba Galadima ya sanar mana cewa lallai akwai abu mai kamar haka da zai faru amma dai baya so ya fadi abin kafin a bayyana shi.
Bayanai sun nuna cewa hakan na da nasaba da shirin da wadannan gungun jigajigan ‘yan siyasa komawa jam’iyyar PDP domin tunkarar Buhari da makarraban sa a 2019.
Idan ba a manta ba tun bayan rantsar da wannan gwamnati ne ake ta takun saka tsakanin shugaban kasa da wadannan jiga-jigan yan jam’iyyar wanda da yawa daga cikin su sun koka ne kan watsi da su da aka yi da kuma nuna halin ko in kula da jam’iyyar tayi musamman shugaban kasa.
A makon da ya gabata tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa shi kadai tal, da jam’iyyar PDP za su iya kada Buhari, wanda a martanin da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya fitar daga baya kuwa ya bayyana cewa ko karamar hukumar sa ma ba zai iya kawo ba a 2019.
Yanzu dai kungiyar da nan tana ganawa a tsakanin mambobin ta da sauran ‘yan jam’iyyar APC da ke cike fam da fushi kan yadda aka mai dasu saniyar ware.
Discussion about this post