A ranar Talata ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zama cikakken ma’aikacin jami’ar da ake karatu daga gida wato wato National Open University of Nigeria, NOUN.
Obasanjo ne dalibi na farko da jami’ar ta ba shaidar kammala karatun digirin-digirgir wato Phd wanda bayan haka ta bashi aiki.
Obasanjo zai yi aiki ne a ofishin makarantar dake jihar Ogun.
Mai kula da aiyukan makarantar a jihar Ogun, Ibrahim Salawu, ya zazzagaya da Obasanjo makarantar sannan ya nuna masa ofishin sa.
Obasanjo ya jinjina wa jami’ar sannan kuma ya ce zai yi aiki tukuru domin ci gaban jami’ar.
