Akalla mutane 500 ne suka canza sheka daga PDP zuwa APC a jihar Legas

0

A ranar Talata ne daruruwan ‘yan jam’iyyar PDP suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar Legas.

Mutanen dai sun fito ne daga mazabu da gundumomi 57 dake jihar.

Jagoran masu canza shekan, Elijah Awodeyi ya bayyana cewa sun yi haka ne ganin irin dinbin nasarorin da ake samu a karkashin mulkin APC musamman a jihar.

Ya ce ” Tabbas ana kwankwadan romon dimokradiyya a jihar Legas karkashin mulkin APC, wato mulkin Ambode, kaga ko me zamu ci gabada yi a PDP.”

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Legas Tunde Balogun ya yi wa masu canza shekan maraba sannan yace yana taya su murna da Allah ya fidda su daga duhu zuwa haske.

” Muna yi muku maraba, sanna muna yi muku fatan Allheri da kuma ku sakata ku wala a APC abin ku APC naku ne yanzu.

Share.

game da Author