Gwamnatin Tarayya ta raba wa mabukata akalla guda 300,000 naira biliyan 10 ta hanyar tsarin tura musu ta asusun ajiyar su, wato CCT.
Babban Jami’in Kula da Raba Kudaden, Temitope Sinkaye ce ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya haka a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Ta ce an fara wannan shiri tun cikin 2016, kuma da jihohi takwas aka fara wadanda suka cika sharuddan da gwamnatin tarayya ta gindaye.
Sharudda da matakan kuwa inji Sinkaye su ne jiha ta samar da ofisoshin kuda da tafiyar da aiki, samar da ma’aikata da kuma kayan aikin fara raba wa mabukata kudaden.
“Kowace jiha na da hakkin shigar da mabukatan ta cikin tsarin, amma idan ta cika wadancan sharudda da gwamnatin tarayya ta shinfida.
“Amma dai ya zuwa yanzu jihohi 20 ne kadai suka cika wadannan shaurudda.” Inji ta.
Discussion about this post