1 – Da Hakeem Baba Ahmed aka fara yin fadi-tashin kafa jam’iyyar CPC ta kasa bakiya da ta jihar Kaduna.
2 – Hakeem Baba Ahmed ne ya yi shugabancin jam’iyyar CPC na jihar Kaduna.
3 – Hakeem Baba Ahmed ya taka rawar gani wajen kare muradi da mutunci Buhari a siyasar Arewa da kasa baki daya, a lokacin da Muhammadu Buhari ke takara a karkashin jam’iyyar CPC a zaben 2011.
4 – Hakeem Baba Ahmed ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC ‘Maja’ a kasa baki daya.
5 – Hakeem Baba Ahmed ne shugaban jam’iyyar APC na farko a jihar Kaduna.
6 – Ya sadaukar da lokaci da dukiyar sa bakin gwargwado wajen tafiyar ‘Buhariyya.’
7 – Hakeem ya yi rubuce-rubucen kare Buhari a kafafen yada labarai na kasar nan fiye da dubban ‘yan Buhariyya.
8 – Ya sha gabatar da intabiyu ya na maida wa masu sukar Buhari martani a wuraren da wasu suka kasa fitowa su maida raddi a madadin Buhari.
9 – Tun kafin a kai ga kafa gwamnati ‘Guguwar Buhariyya’ ta fara sacce masa tayoyi, aka nisa ana barin sa baya a hanya.
10 – Ya daure an ci gaba da tafiya tare da shi har aka yi zaben Shugaban Kasa na 2015.
11 – Hakeem ne ya kasance Babban Wakilin Muhammadu Buhari a wurin kirga kuri’un zaben 2015 a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
12 – Hakeem ne ya sa hannu a madadin Buhari a gaban Hukumar Zabe, cewa Buhari da jam’iyyar APC sun amince da sakamakon zaben 2015.
13 – Ranar Hayaniya da Hauragiyar Sanata Orubebe a wurin kidayar kuri’a, a Cibiyar Gudanar da Taron Kasa da Kasa, Hakeem Baba Ahmed ne ya tashi ya ragargaji Orubebe, saboda ya nemi ya haddasa rudu a cikin kasa, ganin cewa Buhari ne mafi yawan kuri’u fiye da Goodluck Jonathan.
14 – An bayyana sakamakon zabe, Buhari wanda Hakeem ya kare wa kuri’u daga hayagagar Orubebe ya yi nasara.
15 – An kafa gwamnatin APC har aka gama raba mukamai amma Hakeem ko mukamin goge takalmin Buhari bai samu ba.
16 – Ya hakura da ‘kaddarar siyasa’, ya zauna jiran-tsammani.
17 – Cikin 2017, Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya ji tausayin sa, ya nada shi mukamin Shugaban Ma’aikatan Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa.
18 – An daina jin Hakeem kwata-kwata a cikin APC ko a cikin gwamnati, saboda an ci birni da yaki, ko tukurun bawa bai samu ba.
19 – Ranar 2 Ga Yuli, 2018, ya yi sallama da APC, ya ce ya yi wa jam’iyyar fitar-zarar-bunu.
20 – Misalin abin da APC ta yi wa Hakeem Baba Ahmed ya yi daidai da dalilin da ya sa Bahaushe ke cewa, “Siyasa romon jaba, ga kitse kuma ga wari.”