A yau litinin ne Fadar Shugaban Kasa ta gayyaci Sufeto Janar na ‘yan sanda domin jin dalilin da ya sa wasu zaratan ‘yan sandan Mobal yin zanga-zanga a kan babban titin Maiduguri.
Jami’an dai sun yi zanga-zangar ce tare da wakokin nuna rashin amincewa da ci gaba da rike musu hakkokin su na alawus har watanni shida.
Su tare babban titin Maiduguri zuwa Kano, suka hana motoci wucewa, har sun a rera wakar ‘mun gaji haka nan’ kuma akasarin su dauke da ganyen.
Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa an ga Sufeto Janar Ibrahim Idris na ta sauri zai shiga ofishin shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari.
Rundunar ‘yan sandan kasar nan dai ta fito ta ce ba zanga-zanga aka yi ba, kawai dai sun fito ne su na tambayar yaushe za a biya su alawus din na s.