An samu rudani a safiyar litinin a garin Maiduguri, yayin da ‘yan sandan musamman wadanda da ka tura Maiduguri jihar Barno, suka fito yin zanga-zangar nuna damuwar su kan hana su alawus na watanni shidda da ba a yi ba.
An ce an kwaso ‘yan sandan daga kowace jiha cikin jihohin fadin kasarnan, domin su taimaka a dakile Boko Haram.
Jami’an ‘yan sandan sun kuma rika yin harbi sama, abin da ya janyo masu ababen hawa da matafiya a kasa suka rika shekawa a guje.
Wani jami’in dan sanda da ya ce PREMIUM TIMES ta sakaya sunan sa, ya shaida cewa “Mun gaji da gafara-sa haka nan. Sama da wata shida an kawo mu nan an jibge, babu wurin kwana mai kyau, wani lokaci ma a kwararon cikin gidajen wasu manyan jami’an ‘yan sanda muke kwana, ko mu rika kwana a waje. Saboda haka mun gaji haka nan fa.”
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Barno, Damian Chukwu ya ce ya na sane da jinkirin biyan kudin da ba a yi.
Sai yace hakan na da nasaba da rashin sa wa kasafin kudi na 2018 hannu da wuri.
Discussion about this post