An damke hatsabiban da suka addabi Jihar Zamfara da hare-hare –’Yan sanda

0

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Zamfara, ta bayyana cewa ta damke wasu hatsabiban ‘yan ta’addar da ke kai hare-hare a jihar.

Babban Jama’in hulda da jama’a na ‘yan sandan Mohammed Shehu ne ya bayyana a cikin wata takarda da ya fitar ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar.

Shehu dai bai bayyana sunayen su ba, amma ya ce an damke su ne a kauyen Gurusu, cikin karamar hukumar Bukkuyum.

ABDULAZIZ-YARI Zamfara

Ya ce an samu nasarar cafke su ne bayan samun rahoton cewa makasan sun nufi Gurusu dauke da makamai.

Nan da nan jami’an tsaro su ka dirar musu

“Kwamandan Mobal na yankin Anka, ne da kan sa ya ja rundunar jami’an tsaro zuwa Gurusu, suka shafe awanni hudu suna sintiri a cikin dajin har suka cim masu.’’

Ya ce an kuma same su da bindigogi da albarusai

Share.

game da Author