Zan iya sa Shekau da sauran kwamandojin sa yin saranda –Kwamanda Rawana Goni

0

Daga cikin tsoffin kwamandojin Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, mai suna Rawana Goni, ya roki hukumomin tsaro na sojojin Najeriya cewa su kyale shi ya zanta da Shekau ta wayar tarho, domin ya sa shi da sauran kwamandoji akalla 137 su mika wuya, su yi saranda.

Rawana Goni dai a zaman yanzu ya na tsare ne a sansanin tsare masu laifi na sojoji a Maiduguri, inda ake musu huduba da nasihar gyaran hali da tsarkake zukata, ya bayyana haka ne lokacin da ya ke zantawa da wakilin Kamfanin Dillancin Labarai, NAN.

Goni dai haifaffen garin Bama ne a cikin jihar Barno, kuma ya mika wuya ne ga sojojin Kamaru, bayan ya gudu daga Dajin Sambisa, kimanin watanni takwas da suka gabata.

Ya yi ikirarin cewa shi babban kwamanda ne daga cikin manyan kwamandojin Shekau a cikin Dajin Sambisa.

Rawana Goni ya kara da cewa akalla akwai sansanoni 10 na Boko Haram a cikin Sambisa, ya ci gaba da cewa matsayi na karshe da ya rike kafin ya gudu, shi ne Babban Kwamanda mai sasanta rashin jituwa a tsakanin su.

Ya kuma sasanta rigingimu a tsakanin ma’aurata da sauran rashin jituwar da kan taso a tsakanin iyalai da makwabta.

“Na sha tsirar da rayukan wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, ta hanyar rage musu wa’adin hukuncin da aka yanke musu idan sun aikata laifuka.

“Ina daya daga cikin wadanda ke fada a ji, kuma duk abin da na yanke to ya zauna kenan, domin ana saurare na.

“Na shiga Boko Haram ne saboda matsanancin halin da shiga, cikin shekara biyar da ta gabata. A lokacin da Boko Haram suka mamaye garin Bama, sai na gudu zuwa cikin kasar Kamaru ni da iyali na, tsammanin cewa a can na tsira kenan.

“Amma ina shiga cikin Kamaru sai na fada a cikin sansanin wasu gungun Boko Haram din, wadanda na yanke cewa tabbas ba zan iya tsira daga gare su ba, sai kawai ni ma na shiga cikin su.

“Bayan kwanaki kadan, sai muka bude sansani na dindindin a kan iyakar Kamaru, muka sa wa sansanin suna Aluska, To a wannan sansani ne muka rika yin atisaye da koyon yadda ake sarrafa bindigogi da sauran makami.

“Bayan an gama ba mu zazzafan horo ne sai muka darkaki wani sansanin sojoji inda muka fara kai farmakin mu na farko. Muka fatattaki sojojin nan, muka kwashi dimbin makaman da muke iya kwasa daga cikin rumbun ajiyar makaman su. Amma ba mu dauki motoci ko guda daya ba, saboda wajen kewaye ya ke da ruwa.

“Muka kai wa Shekau makaman da muka kwasho daga sojojin Kamaru. Ya yi ta murna da farin ciki. Ya cika da mamakin yadda mu biyar kacal muka fatattaki karamar rundunar sojoji. Daga nan sai ya nada ni shugaban wannan runduna ta mu, kuma ya maido mana makaman da muka kwaso daga wurin sojojin Kamaru.

“Daga nan sai na gada cikakkar runduna na rika ba su tirenin, saboda a matsayin ka na kwamanda, ana so ka kasance akalla akwai zarata 250 a hannun ka.

“To da wannan zarata 250 ne muka yi wa kauyen Waza, Damaga da Banki dirar mikiya. Daga nan kuma muka dira garin Bama, inda can ne mahaifa ta.

“To zuciya ta ta girgiza matuka, ganin irin yadda aka rika azabtar da jama’ar gari na kuma ana karkashe su, ga mata da kananan yara an bar su cikin radadin kuncin azabar rayuwa.

’‘To daga can ne na isar wa makusantan zarata na 137, cewa mu san dabarar da muka yi muka kubutar da jama’ar mu su tsira daga kurkukun da suke tsare.

“Sai da na yi galabar cetar da mutum 300 da ke tsare a cikin kurkuku a Bama. Na yi wa masu gadin kurkukun karya cewa zan tafi da su ne duk mu kashe su. Amma zan dauke su ne zuwa Konduga, na ce musu kowa ya sulale ya buya domin ya ceci ran sa.

“Wadanda aka kama din aka tsare, an rika gallaza musu, wasu kuma aka rika amfani da su aka koya wa sabbin shiga Boko Haram yadda ake saiti da bindiga ana harbi. Su aka rika jera wa ana saiti, ana dirka masu bindiga domin a koyi saiti.”

Dangane da halin da Shekau ke ciki, Goni ya ce shi dai a iyakar sanin sa lafiya kalau ya ke, ba kamar yadda ake ta yada labaran kad-da-kanzon-kurege ba.

Ya ce abinda kawai ya sani shi ne shekaru kamar biyar baya ya ji ciwo a kafa, bayan da ya hau kan doki ya fado.

Ya yi amanna cewa za a iya kawon karshenn yakin idan aka bari yayi magana da Shekau ta wayar tarho. Ya ce ya na so ya shaida wa Shekau da sauran mukarraban sa cewa ya na raye.

“Zaratan yara na 137 na nan a Sambisa, suna jiran su yi cewa ina nan a raye ba a kashe niba. ina tabbatar muku da cewa idan suka ji haka su ma za su fito daga cikin Sambisa, saboda na sha ce musu mu gudu, amma suna cewa idan suka fito kashe su za a yi. Amma ni sai na ce musu saranda zan yi, kuma ba za a kashe ni ba. Idan suka ji ba a kashe ni ba, su ma mika wuya za su yi.”

Goni ya gode wa sojojin Najeriya dangane da irin kulawar da suke ba ‘yan Boko Haram wadanda suka mika wuya.

Share.

game da Author