2019: Kwankwaso ko karamar hukumar sa ba zai iya kawo ba ballantana ya ja da Buhari a Kano – Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa babu ta inda tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso zai sake yin tasiri a jihar Kano wai har ya ja da Buhari.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammed Garba ne ya fadi haka a wata takarda da ya saka wa hannu a madadin gwamna Ganduje.

Ganduje ya ce duk kayan yakin sa da yake takama da su a Kano an karya su basu da tasiri yanzu ko a jihar Kano.

” Kwankwaso bashi da madafa yanzu sannan ba shi da kaifin kwakwalwa da hikimar da zai iya jan ragamarar Najeriya kamar yadda ake gani.

” Shekarun sa uku kenan a majalisar dattawa bai taba kirkiro koda kudiri daya ce domin mutanen sa, sannan bai yi wa mutanen sa aikin azo a gani ba koda guda daya ce har yanzu.

” A tsawon wannan shekaru bashi ma a garin na Kano, mu kuma muna gari muna ta murza siyasa kamar yadda ya kamata a jihar.

” Nemar PDP ta tsayar da shi mafarki ce yake yi kawai domin buri ce da bazai taba dacewa da ita ba. PDP ba za ta manta da irin abin da yayi mata ba.

” Ina mamakin yadda wai yanzu Kwankwaso ne ke maganar Ibrahim Shekarau, mutumin da ya wulakanta, sannan kuma wai PDPn da ciwa mutunci yanzu.

” Kwankwaso kuranta kan sa kawai yake yi amma bashi da tasiri yanzu a siyasar Kano, an riga an rugurguza duk wani abin da yake takama da shi a Kano sannan kuma ya sani ma Buhari ba sa’an sa bane yanzu idan ma haka ya ke tunani.

Share.

game da Author