INEC za ta bayyana binciken zaben yara a Kano

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, yac bayyana cewa nan ba da dadewa ba INEC za ta fitar da sakamakon binciken zargin jefa kuri’ar da ake cewa kananan yara sun yi a zaben kananan hukumomin Kano.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da editocin labaran siyasa na kafafen yada labaran kasar nan a Lagos.

Yakubu ya jaddada musu cewa tun farko ya fada cewa ba da rajistar masu kada kuri’in Hukumar Zabe ta Kasa aka yi zaben Kananan hukumomin Jihar Kano ba.

Duk da haka ya ce saboda yawan tambaya da bukatar da jama’a ke yi kan sakamakon binciken, INEC za ta fitar da binciken na ta kan wannan zaben da hukumar zaben jihar Kano, KANSIEC ta gudanar a cikin watan Fabrairu na wannan shekara.

“INEC ta gudanar da binceke, an kawo mana sakamako, kuma mun kira taron ‘yan jarida, mun shaida musu cewa babu wata alaka tsakanin zaben kananan hukumomin jihar Kano da INEC.

“Binciken da INEC ta yi ya tabbatar da cewa mazabu da yawa ba a ma yi amfani da rajistar zabe ba domin tantance masu kada kuri’a na aihini. Kawai sun gudanar da zaben ‘yan awon-igiya ne, ta-ci-barkatai.”

Ya tabbatar da cewa zai karfafa matakan sabunta rajista domin kara samun inganci da sahihancin zaben 2019.

Bayan kammala binciken da INEC ta gudanar, Yakubu ya fitar da wata makara wadda shi da kan sa ya rubuta a farkon watan Mayu, kuma aka buga a cikin jaridun kasar nan.

Daga cikin bayanan da ya yi domin wanke INEC daga zargi, shugaban na INEC ya ce:

“Jama’a su fahimci cewa INEC ba ta kafa kwamitin binciken ta wai don ya binciki yadda KANSIEC ta gudanar da zaben ta na Kananan Hukumomin Kano, ko don gano matsalolin da aka fuskanta a lokacin zaben ba. INEC a dokance ma ba ta da ikon yin haka. Kawai abu daya ne aikin Kwamitin Bincken da INEC ta kafa. Aikin kuwa shi ne ya gano shin ko akwai sunayen kananan yara a cikin Sunayen Rajistar Zabe wanda INEC ta bai wa KANSIEC, ko a’a?

“Wannan kwamitin bincike kuwa ya kunshi Kwamishinan Zabe Na Kasa, Injiniya Nahuce a matsayin Shugaba, Kwamishinonin Yanki biyu, Barista Mike Igini da Kassam Geidam, da kuma wasu Daraktoci da ma’aikaikatan Hukumar, wadanda kwararru ne wajen zakulo binkike a na’urori. Kuma tuni kwamitin ya gabatar da rahoton sa. INEC ta yi nazarin rahoton kwamitin a tsanake, kuma ta gamsu da sakamakon rahoton kwamitin.”

Share.

game da Author