Zargin Daddatse Kasafin 2018: Shehu Sani ya yi wa Buhari gar-da-gar

0

Sanata Shehu Sani da ke wakiltar Shiyyar Kaduna ta Tsakiya, ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari gar-da-gar, dangane da yadda shugaban ya nuna fushi da yadda Majalisar Tarayya ta zaftare wasu ayyuka, kamar yadda ya yi ikirari.

A cikin wani jawabi da ya aika a shafin sa na Facebook, Sanatan ya cika da mamaki, har ya nuna mamakin yadda Buhari ya yi kasassabar sa wa kasafin hannu matukar dai har ya na da korafi a kan sa.

“Giribtun me Shugaban Kasa ke yi da har zai yi karkarwar saka wa kasafin hannu idan bai yarda da shi ba? Shi ne fa ake buga wa tambarin aiki da gaskiya da aiki kan abin da ke daidai. Tunda ya na zargin kasafin cike ya ke da asarkala, barankyankyama da harkalla, me ya kai shi saka hannu ya zama doka?”

Sanatan ka kara nanata cewa, “Wane mahaluki ne ke da karfin fada-a-ji kan Shugaban Kasa da har ya tirsasa shi ya sa hannu a kan a bin da ya ke ganin kuskure ne?”

“Kwamitin Duba Kasafin Kudi ya fito karara ya bayyana wa duniya cewa an yi gyare-gyaren ne da sanin ministoci. Me ya sa har yau babu wani minista da ya fito ya karyata majalisa? Idan kuma ba da sanin Shugaban Kasa ministoci suka amince da gyare-gyaren da majalisa ta yi ba, me ya sa har yau bai kore su ba?”

“Ina tabbatar da cewa wadanda suka fi dacewa su yi magana a majalisa, za su fito su maida wa shugaban kasa raddi daya-bayan-daya. Domin haram ne kawai daga jama’a sun ji ba’asin bangare daya sai su yi gaggawar yanke hukunci kawai.

“Idan Shugaban Kasa har bai yarda da kasafin ba, bai kamata ma kwata-kwata ya sa masa hannu ba, sannan daga baya ya fito ya na bobbotai. Saka hannu a abu ya na nufin amincewa da abin har zuci, ba tare da wata inda-inda ba. Ba a sa hannu a bisa tilas.’’

Share.

game da Author