Za a biya ma’aikata albashi kafin Sallah a jihar Kebbi

0

Sakataren yada labarai na gwamnatin jihar Kebbi Abubakar Dakingari ya bayyana cewa gwamnati za ta biya duka ma’aikatan jihar, da kananan hukumomi albashin su kafin bukin karamar sallah.

Dakingari ya sanar da haka nejim kadan bayan gwamnatin tarayya ta sanar da ranakun Juma’a da Litini hutun karamar sallah.

A nashi tsokacin sakataren gwamnatin jihar Babale Yauri yace gwamnati ta yi haka ne domin mutanen jihar su sami damar yin shagalin sallar Eid-El-Fitr tare da ‘yan uwa da abokan arziki cikin walwala da kwanciyar hankali.

Ya ce gwamna Abubakar Bagudu na wa kowa barka da Eid-El-Fitr.

Share.

game da Author