Wasu hasalallun matasa sun banka wa motar jami’an kwastam wuta bayan ta haddasa hadarin mota.
Ibtila’in ya faru a garin Uya-Oro da ke cikin Karamar Hukumar Oron ta jihar Akwa Ibom.
Mafusatan kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito, sun banka wutar ne bayan da wata mota mai dauke da shinkafa wa kwastam suka biyo, ta murtsike wasu mutane uku da ke kan babur din ‘yan acaba .
Wanda aka yi abin kan idon sa, ya ce daya daga cikin fasinjan ya mutu nan take, saura kuma sun ji mummunan ciwo.
Hadarin dai ya faru a ranar Alhamis misalin karfe uku na rana.
Kakakin Yada Labarai na ‘yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce jami’an kwastan ne suka biyo direban motar da ke dauke da shinkafar, har suka dirka harbi domin ya tsaya.
Maimakon direban ya tsaya sai ya kara wuta, har ya banke wadanda ke kan babur din.