Yadda Gwamnatin Buhari ta ja wa Najeriya asarar naira tiriliyan 2.7

0

A ranar Talata ne wata Kotun Gundumar Washington DC da ke Amurka ta yanke hukuncin dalar Amurka biliyan 6.59 a kan Najeriya.

Ba wadannan makudan kudade na fitar hankali ne kadai diyyar da aka dora wa Najeriya ba, har da bi-ta-da-kullin karin wasu daloli biiyan 2.30 da mai shari’a ya ce sai Najeriya ta biya a matsayin kudin-ruwa.

Alkali ya yanke wannan hukunci ne bayan da Najeriya ta kasa bayyana a gaban mai shari’a domin ta kare kan ta.

Idan aka kwatanta kudaden da Najeriya ta yi asara sakamakon wannan hukunci da aka yanke a ranar Talatar da ta gabata, sun kai naira tiriliyan 2.7. Wannan fa idan aka canja duk dalar Amurka a kan naira 306 kenan.

Yayin da mai shari’a ya yanke wannan hukunci, PREMIUM TIMES ta gano cewa idan da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi aiki ko ta yi amfani da kudirorin da Gwamnatin Goodluck Jonathan ta zartas kan lamarin, to abin da za a biya a matsayin diyya bai kai kashi 10 na dala biliyan 8.9 ba.

Amma maimakon Gwmnatin Buhari ta yi amfani da abin da Gwamnatin Jonathan ta zartas, sai ta buge ta na bata lokaci da kuma jan-kafa wajen tozarta gwamnatin Jonathan ta na gwasale yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin da Buhari ya gada din da kamfanin Process & Industitial Development Limited.

Wannan kamfani wato P&ID, wani kamfanin injiniyoyi ne masu yin kwangiloli ne mai karfin gaske a Amurka.

P&ID ya zargi Najeriya da laifin karya yarjejeniyar ayyukan kwangila da suka cimma amincewa tsakanin su da juna.

Kwafen takardun bayanan da ke a hannun PREMIUM TIMES a yanzu haka, sun tabbatar da cewa gwamnatin Jonathan ta kafa kwamiti wanda ya samu nasarar zaman cimma yarjejeniyar amincewa da P&IP cewa bangarorin za su sasanta a waje ba a gaban kotu ba.

An cimma yarjejeniyar cewa Najeriya za ta biya diyyar dala milyan 850 kadai, wato kashi 9.6 na kudin kwangilar, wanda ya tashi gabadaya a kan naira biliyan 8.9.

Maimakon Gwamnatin Buhari ta cika sharuddan yarjejeniyar, sai ta umarci lauyoyin ta cewa a sake komawa kotu domin ta kalubalanci shari’ar, wato ba za ta biya kudin ba kenan wanda gwamnatin Jonathan ta amince Najeriya za ta biya.

Yayin da aka koma kotu, maimakon Najeriya ta yi nasara, kamar yadda gwamnatin Buhari ya bugi kirjin cewa za ta samu a kotu, sai kotun ta yanke hukuncin da bai yi wa gwamnatin Najeriya dadi ba.

Hukuncin ya nuna cewa tunda har Najeriya ta ki biyan dala milyan 850 da aka sasanta cewa za ta biya ba tare da an gurfana a gaban shari’a ba, to a yanzu kuma dala bilyan 6.6 za ta biya kamfanin diyya.

Kamfanin dai a Tsibirin British Virgin Island ya ke.

Bugu da kari kuma, an kara lafta wa gwamnatin Najeriya wata diyya har ta dala biliyan 2.3 a matsayin hukuncin bata lokacin shekaru biyar da ta yi na kin biyan kudin da aka cimma yarjejeniya tun da farko.

Wannan jangwangwama dai ta afka wa Najieriya ne bayan samun sabanin wata kwangila tsakanin Kamfanin Man Fetur na Najeriya, wato NNPC ya yi da kamfanin na P&ID.

Wadanda su ke da cikakkiyar masaniyar rikicin, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana kusa da saukar gwamnatin Jonathan ne ta amince za ta biya P&ID diyyar dala milyan 850.

Da ya ke a lokacin gwamnatin ta kusa sauka, sai hakkin biyan kudin ya koma kan gwamnatin Muhammadu Buhari, tunda ita ce ta gaji gwamnatin Jonathan.

Wata majiya mai tushe ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa, “Gwamnatin Jonathan ta amince za ta biya diyyar dala miliyann 850, amma ba ta sa hannun amincewa da biyan ba, ganin cewa saura ‘yan kwanaki gwamnatin ta sauka. Ta yi haka ne don kada a zarge ta da harkalla.”

BATA LOKACIN DA YA JANYO WA NAJERIYA MATSALA

Akwai lokacin da a zaman sauraren shari’ar har lauyan Najeriya mai suna Supo Shasore ya shawarci Najeriya cewa hujjojin fa Najeriya ta rike a matsayin dalilan kin biyan diyyar dala milyan 850 ba masu karfi ba ne.

Shasore ya shawarci Najeriya cewa gara fa a yi mai yiwuwa, domin ya na gudun kada can gaba cibi ya zama kari.

To a ranar 11 Ga Agusta, 2014, sai Ministan Shari’ar Najeriya na lokacin, Mohammed Adoke ya shawarci gwamnatin lokacin da ta dauki matakan fara biyan kudin domin a samu hanyar fara yayyafa wa kakudubar rikicin ruwan sanyi.

A karshe dai an cimma cewa gwamnati ta amince za ta biya dala bilyan daya da rabi.

Shugaba Goodluck Jonathan a lokacin ya kara matsa lambar cewa a roki kamfanin ya kara sassauta wa Najeriya. A karshe dai aka cimma yarjejeniya ta karshe cewa to Najeriya ta rungumo dala milyan 850 ta biya kawai, domin a bar maganar, a rufe shafin rikicin kawai.

An cimma wannan yarjejeniya ta karshe a ranar 29 Ga Afrilu, 2015, cewa za a biya dala milyan 850, wato ana saura wata daya kacal gwamnatin Jonathan za ta sauka.

Gwamnatin Jonathan ta amince za a biya kudin, duk kuwa da cewa ba haka ta so ba. Gwamnati a lokacin ta so a ce dala milyan 500 ne za ta biya, ko ma kasa da haka.

Daga nan kuma sai aka kulla cewa za a fara da biyan dala milyan 100, jim kadan bayan cimma yarjejeniyar, daga nan kuma sai a datsa sauran kudin zuwa kashi uku.

Hakan ya na nufin duk bayan watanni hudu Najeriya za biya dala milyan 250 kenan ga kamfanin na P&ID.

Daga nan kuma sai Ministar Harkokin Kudade, Diezani Alison-Madueke ta rubuta wa Goodluck Jonathan wasika cewa ya amince Kamfanin NNPC ya biya kudaden da za a fara biyan diyya ga kamfanin kwangilar.

To a ranar 25 Ga Mayu, 2015, kwanaki hudu kafin saukar Jonathan, sai ya maida wa ministar amsar cewa, “Ba zan iya sa hannu a wannan kurarren lokaci ba, sai dai a mika wannan bukata ga gwamnati mai jiran gado domin su rattaba amincewar biyan kudin.”

PREMIUM TIMES ta samu kwafen wasikar da Jonathan ya aika wa Diezani, kuma ta samu kwafen wacce ita ministar ta fara aika masa mai dauke da neman fara biyan kudaden a ranar 18 Ga Mayu, 2015.

Sai dai kuma jim kadan bayan hawan Gwamnatin Buhari, washegari a ranar 30 Ga Mayu, 2015, an gabatar da matsalar a gaban Buhari da Osinbajo, inda su kuma suka jajirce cewa da a biya kudin har gara a sake sabuwar yarjejeniya kawai.

Nan da nan sai gwamnatin Buhari ta maye gurbin lauyan Najeriya Shasore da wani lauyan daban, mai suna Bolaji Ayorinde.

Dukkan su dai Bolaji din da kuma lauyan farko Shasore, duk manyan lauyoyi ne masu lakabin ‘SAN’.

Daga nan aka umarci Bolaji Ayorinde da ya ci gaba da bin ba’asin shari’ar a kotun London.

A kan haka ne a ranar 25 Ga Disamba, sai sabuwar gwamnatin Najeriya ta nemi kotun da cewa ta jingine waccan yarjejeniya da aka kulla da gwamnatin Jonathan kawai, ba za ta biya diyyar ta dala milyan 850 ba.

An ci gaba da sa-toka-sa-katsi a kotu, inda a karshe kotu ta yi watsi da bukatar gwamnatin Najeriya, har dai aka kai ga yanke hukuncin da ya janyo wa Najeriya yin mummunan da-na-sani, wanda aka ce keya ce, daga baya ta ke.

KWANGILAR DA TA ZAME WA NAJERIYA ALAKAKAI

An kulla wannan kwagila ce a tsakanin kamfanin P&ID da kuma Hukumar NNPC a madadin gwamnatin Najeriya.

An amince da cewa P&ID zai gina katafaren aikin Iskar Gas a Adiabo da ke cikin karamar hukumar Odukpani a Jihar Cross River.

Gwamnatin laokacin ta shirya kwangilar ce da nufin gina aikin samar da iskar gas wanda zai rika zama a matsayin abin wadatar da makamashi da kuma hasken lantarki a Najeriya.

Bayan kammala wannan rahoto, PREMIUM TIMES ta tuntubi ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, amma kakakin sa Laolu Akande ya ce wannan magana ai Antoni Janar na Tarayya, wanda kuma shi ne Ministan Shari’a za a tuntuba.

An kira wayoyin sa bai dauka ba, kuma an yi masa sakon tes, amma bai maida amsa ba.

Sai dai kuma a yayin jin ta bakin sa, Karamin Ministan Man Fetur, Ibe Kachikwu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana nan ana wani abu akan wannan hukunci da ka yanke kan Najeriya.

Share.

game da Author