Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa akalla Boko Haram da Sojojin Najeriya sun kashe kananan yara 881, a fadan katilan-makatulan da aka gwabza tsakanin bangarorin biyu, a cikin 2017 kawai.
Daga cikin wadannan adadi, an tantance cewa yara 235 an kashe su ne a wani hari bisa kuskure da sojoji suka kai wa sansanin gudun hijira na Rann, a cikin jihar Barno.
Harin dai an kai shi a bisa kuskure da hanyar jefa bam daga jirgin yaki a sama.
An kuma kashe wasu 26 da aka bude wa wuta bayan da aka zarge su dauke da bama-bamai a jikin su, duk a cikin 2017.
Wadannan bayanan duk su na kunshe ne a cikin rahoton Babban Sakataren Majalisar da aka gabatar a kan makomar yara kanana a yankin da ake yaki.
Rahoton ya kuma tabo wadanda aka kashe a Afghanistan, India, Philipines, Syria da Yemen.
Rahoton ya koka a kan yadda ake koya wa yara horon kai hare-hare a makarantu, asibotoci da sauran wurare.
Gaba daya dai Majlisar Dinkin Duniya ta ce an samu rahoton gallazawa da tauye wa kananan yara harki har 21, 000 a tsakanin Janairu zuwa Disamba, 2017, idan aka kwatanta da 15,000 da aka samu rahoto a cikin 2016.