Gwamnatin Najeriya ta kara tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saman kasar, biyo bayan barazanar da aka ce rikakkun ‘yan ta’addar ISIS suna shirin dana wa jiragen fasinjoji bama-bamai.
Duk da cewa dai har zuwa yanzu babu wata kwakkwarar barazanar da aka ci karo da ita, kuma gwamnatin tarayya ba ta ce an fuskanci wata barazana kai-tsaye ba, rahotannin na tabbatar da cewa ana samun fantsamar ‘yan kungiyar ISIS da ke shiga Najeriya daga Iraq da Syria da sauran kasashen Gabas ta Tsakiya.
Zai iya yiwuwa sakamakon wannan rahoton ne aka kara inganta tsaro a filayen jiragen.
Ofishin Sakataren Gwamnantin Tarayya ne ya ankarar da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Najeriya, Hukumar Kula da Sararin Saman Najeriya, da kuma Hukumar Kwastan ta Kasa cewa tun a cikin watan Afrilu ISIS ta yi wannan barazana.
Ofishin na Sakataren Gwmnatin Tarayya ya aika musu da kwafen takardar gaggauta daukar matakai a ranar 25 Ga Mayu, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ci karo da kwafwen takardar.
Takardar dai ta nuna cewa babu wata alaka ta kai-tsaye da wasu kungiyoyin tsatstsauran ra’ayin addini ta Afrika, amma ana ganin fantsamar ‘yan ISIS a cikin Afrika da kuma alakar da ake ganin akwai tsakanin ISIS da bangaren Boko Haram da ke karkashin jagorancin Abu Musab Al-Barnawi, ka iya sa a kara matakan tsaron.
Binciken da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ke kafa hujja da shi, bai wuce inda a ranar 22 Ga Afrilu, kakakin ISIS, Abu Hassan Al-Muhajir ya bayyana cewa, “za mu zubar da jinainai a bisa sararin samaniya” ba.
ISIS dai a baya sun bayyana alhakin kakkabo jirgin Rasha, wanda ya fado ya kashe fasinjoji 224 a cikin 2015.
Discussion about this post