A hira ta musamman da jaridar PREMIUM TIMES tayi da mai ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Kawu Sumaila, ya bayyana cewa tabbas an tirsasa wa Buhari ne ya saka hannu a kasafin kudin 2018 amma ba haka yaso ba.
“ Idan ka duba tun a watan Nuwambar 2017 Buhari ya mika wa majalisar tarayya kasafin kudin 2018 amma kana gani da idanuwar ka sai bayan watanni bakwai sannan suka gama aiki akai. Idan Buhari yace zai maida kasafin kudin zuwa ga majalisar, Allah kadai yasan lokacin da za su dawo masa da shi ya sa ka hannu. Haka ne ya sa dole ya rattaba hannu a kasafin kudin.
“ Duk da cewa majalisa na da ikon jirkita kasafin kudin yadda suke so kamar yadda doka ta ce, haka doka ta ba shugaban kasa damar shima ya kirkiro ayyuka da bayanai kan yadda za a kashe kudin kasa sannan ya mika wa majlisa domin su duba. Wannan shine babban dalilin da ya sa kowani shugaba yake son ‘yan jam’iyyar sa su zamo sune masu rinjaye a majalisa.”
Da aka tambayi Hon Sumaila game da korafin da akeyi cewa ba a iya aiwatar da kasafin kudin kasar nan ba ta yadda zai yi wa mutane tasiri, ya kuranta gwamnatin Buhari cewa, itace gwamnati ta farko tun bayan dawowa mulkin dimokradiyya a kasar nan a 1999 aka iya yin ayyukan dake cikin kundin kasafin kudin har kashi 75 bisa 100.
“ A zamanin mulkin PDP ba a taba aiwatar da ayyuka da ya kai kashi 50 bisa 100 da aka aiyyana su a kundin kasafin kudin kasa ba.”
Sannan kuma yace rashin jituwa da ake samu tsakanin fannin zartarwa da majalisa siyasa ce kawai ba wani abu. Cewa idan zabe ya zo za kaga ana samun irin wadannan rashin jituwa aka-akai.
“ A majalisar wakilai, Buhari na da rinjaye na masu goyon bayan sa. Wannan ko shakka bani da shi akai.
“ Sannan kuma ya kamat a sani cewa dama ba komai bane majalisa za ta amince wa fannin zartarwa, wato gwamnati, za a na samun rashin jituwa a wasu batutuwan.