TAMBAYA: Menene ya ke kai ga a kashe musulmi ko Wanda ba musulmi ba a Shari’a

0

TAMBAYA: Menene ya ke kai ga a kashe musulmi ko Wanda ba musulmi ba a Shari’a

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Inna Lillahi wa inna Ilaihi Raji’una, Lallai rai a gurin Allah tanada daraja kuma Allah ya haramta kashe ta, duk wanda ya kashe rai, ba tare da hakkiba, Allah ya tsinemasa, kuma Allah yana fushi da shi, kuma yayi masa tanajin azaba mai tsanani, sannan kuma a cikinta zai dawwama. Hadisi ya inganta daga Annabi SAW duk wanda ya taimaka wajen kasha wata rai, to ba zai ji kanshin Aljannaba ko ba zai samu rahamar Allah ba. Hakika halin kunchi da muke ciki a duniyar Najeriya ta yau,
baya rasa nasaba da kisan rayukan da ba suji ba, ba su gani ba. Allah ya shiryemu.

Rayuwar musulmi da na wanda ba musulmi ba, duk rayuka ne masu alfarma a waje Allah SWT. Kuma Allah ya hana kashe ko wace irin rai ne ba tare da hakki ba. A musulunci hukama kadai ta keda hurumin kissa idan hukunci ya tabbata cewa mutum yayi daya daga abubuwa masu yawa, ga kadan daga cikin wanda nassi ya zo da su:

1) Idan mutum ya kashe wani kisan ganganci, to shi ma Shari’ah zata kashe shi.

2) Idan mutum ya bada hadin kai ko goyon baya ko ya taimaka wajen kashe wani, kuma Shari’ah ta zartar masa da hukuncin kisa.

3) Ma-auraci kuma ma-zinacin da Shari’ah ta yanke masa hunkun kisa.

4) Riddajen Musulmin da Sari’ah ta yanke masa hukuncin ridda.

5) Dan fashin da shari’ah ta zartar masa da hukuncin kisa.

6) Dan ta’addan da ke kashe mutane da makami, bindiga, ko bam, ko kwaya da sauran muyagun yanyoyin ta’addancin da Shari’ah ta bayyana.

7) Mai Luwadi da wanda ake yin luwadin da shi.

8) Mutumin da ya hana zakka.

9) Mutumin da yabar Sallah.

10) Mutumin da yayi tawaye ga shugaban da al’umma suka yiwa Mubaya’ah.

11) Mutumin da ya jakoranci tawaye ga shugaba.

12) Idan aka yiwa mutane biyu Mubaya’ah, to akashe danyan su idan suka ki dai-daitawa.

13) Mutumin da yaraba kan al’umma.

14) Mutumin da yake fasadi kuma yana yada shi abayan kasa.

A karshe, dukkan abinda hukuma ta yanke hukuncin kisa akai, to ya zamo dalili na kashe mutumin da ya taka wannan hukunci. Allah shi ne mafi sani.

Ya Allah! Ka taimaki shugabanni da hukumomi wajen tsare rayukan al’umma da dukiyar su. Amin.

Share.

game da Author