Sanata Shehu Sani da ke wakiltar Shiyyar Kaduna ta Tsakiya, ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC, ya na mai bada dalilin yadda uwar jam’iyyar ta kasa magance zazzafar rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar shekaru uku bayan ta kafa mulki.
Shehu Sani, wanda ba ya gajiya sukar lamarin irin yadda ake tafiyar da jam’iyyar ta su ta APC, ya bayyana jihohin da ke cikin kakadubar rikici da suka hada da Kaduna, Kano, Bauchi, Kogi, Rivers da wasu jihohin kasar nan.
Jihohi da dama da ke karkashin APC dai ‘ya’yan jam’iyyar na cikin rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa, har ta kai za a zo ga taron gangamin zaben shugabannin jam’iyya nan ba da dadewa ba.
Duk da a cikin watannin baya, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Bola Tinubu domin ya jagoranci sasanta bangarorin APC da ba su ga-maciji da juna, har yau bai yi wani abin a zo a gani ba.
Sanata Sani ya yi bayanin ne a wata hira da ya yi da manema labarai a gidan sa na Kaduna, a lokacin hutun Sallah, ranar Litinin.
Ya ce zaben shugabannin APC da aka yi na jihohi, an gina shi ne a kan tubalin toka.
“Akasarin jihohin kasar nan bulkara kawai aka yi, ba zabe ba. Gwamnonin jihohin da ke APC ne kawai suka rika cire sunayen ‘yan takarar da ba su goyon baya, suka rika dora yaran su.
“Makaryaci ne kawai zai ce an yi zaben shugabannin jam’iyyar APC a Kaduna da wasu jihohi. An dai tara magoya bayan gwamna da gwamnati, suka yi abin da suka yi, daga nan suka fito suka ce sun yi zabe.”
An dade dai ana takun-saka tsakanin Sanata Sani da Gwamna El-Rufai, har ta kai su ga kowa ya maka kowa kotu.
Sanatan yace abin da APC ke yi a yanzu, shi ne dai abin da ta ke aibata PDP da shi baya.