RIKICIN FILATO: ‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 86

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da gano gawarwaki 86 daga asarar rayukan da aka yi a jihar Filato.

Rikici ya barke ne bayan da rahotanni suka bayyana cewa wasu mahara ne suka kai wa masu zaman makoki hari a ranar Asabar da ta gabata a Barikin Ladi.

Wannan ya haifar da harin daukar fansa a cikin garin Jos, musamman a bangaren Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

Hakan ya sa gwamnatin jihar Filato ta kafa dokar-ta-baci a kananan hukumomi uku.

‘Yan sanda sun ce ann kashe mutum 86, an ji wa 6 rauni, an kona gidaje 50, Babura 15, sannan kuma an kone motoci biyu.

Haka kakakin ‘yan sandan Filato, Terna Tyopev ya bayyana.

Share.

game da Author