Ranar Litinin ne Shugabannin bangaren Sabuwar PDP da ke cikin jam’iyyar gambiza ta APC, sun janye daga zaman sulhun da suke yi da gwamnatin Muhammadu Buhari.
A cikin wata takarda sa Shugaban na Sabuwar PDP, Kawu Baraje ya sa wa hannu, ta ce sun yanke shawarar janyewar ne, biyo bayan irin halin bi-ta-da-kullin da ake yi wa mambobin APC da ke cikin bangaren su.
Baraje ya zargi Fadar Shugaban Kasa da yin baki-biyu da kuma harshen-damo.
Sannan kuma ya ce bangaren na su bai yi amanna da imanin riko da gaskiyar bangaren gwamnati ba dangane da yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin su.
Ya bayar da misalin irin gayyatar da aka yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki zuwa hedikwatar ‘yan sanda, inda aka danganta shi da fashi da makami.
Ya ce wannan daya ne daga cikin irin fuska-biyun da gwamnatin Najeriya ke nunawa, kuma hakan ya sa ita gwamnatin ba abar bai wa amana ba ce.
Su dai Sabuwar PDP, su ne wadanda jam’iyyar APC ta taka gadon bayan su har ta samu nasarar cin zabe a karkashin dan takara Muhammadu Buhari.
Buhari ya shafe zango uku ya na takara kuma ya na faduwa. Bai samu nasara ba sai da ya hada baki da Sabuwar PDP, wadanda suka balle daga cikin jam’iyyar PDP suka koma APC gab da zaben 2015.
Akasarin ‘yan PDP da suka taimaka wa Buhari ya hau mulki, duk sun raba hanya da shugaban, wanda ake kallon cewa tun bayan hawan sa mulki ya fi daukar kabilar Yarbawa ya na goyawa a bayan sa, a matsayin ‘yan lelen gwamnatin sa, musamman wajen raba manyan mukaman gwamnati.
YADDA APC TA HAU MULKI A 2015
Tun daga zaben 2003 Muhammadu Buhari ya fara fafutikar neman zama shugaban kasa amma bai yi nasara ba. Ya jaraba a 2007, kuma ya kara jarabawa a 2011 duk bai yi nasara ba.
A zaben 2011 ne shi da magoya bayan sa suka yi zargin cewa PDP ta yi magudi abin da ya haifar da mummunan rikici a wasu manyan garuruwan Arewacin kasar nan, har ta kai ga kona gidajen manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP a garuruwa da dama.
Buhari ya fito ya bayyana cewa ya daina tsayawa takara. Sai dai kuma bayan matsin-lambar da ya fuskanta, ya amince zai sake takara.
A wannan karo, shi da mabiyan sa sun fuskanci cewa idan jam’iyyun adawa ba su yi wa PDP taron dangi ba, to yin galaba a kan ta abu ne mai wuya.
Wannan ya sa jam’iyyar CPC ta Muhammadu Buhari wadda suka kafa bayan ya fice daga ANPP, ta mika goron gayyatar yin gamin-gambiza ga ACN ta su Bola Ahmed Tinubu, APGA da wasu kananan jam’iyyu.
Sun taki babbar sa’a PDP ta afka cikin mummunan rikicin da wasu fitattun gwamnonin jam’iyyar da sauran manyan jam’iyyar sun samu kan su cikin halin kazamin rashin jituwa tsakanin su da Shugaban Kasa na lokacin, Goodluck Jonathan.
Wadannan Gwamnoni tare da gaggan jam’iyya irin su Atiku Abubakar da wasu tsoffin gwamnoni da ke Majalisar Dattawa suka fice daga PDP, suka koma APC.
Wannan ya kara wa jam’iyyar karfi, karsashi, tagomashi da kuma fadada mata kirjin yin karon-battar-karfi tsakanin ta da PDP da ke mulki a lokacin.
FASALIN FUSKAR APC KAFIN ZABE DA BAYAN ZABE
A gefe daya akwai mambobin jam’iyyar CPC, ta su Buhari bayan ficewar sa daga ANPP. Cikin APC akwai Gwamna Almakura na jihar Nassarawa, wanda shi kadai ne CPC ta ci riba, a takarar da ta yi a zaben 2011.
Akwai kuma irin su Aminu Waziri Tambuwal, wanda a lokacin ya na Kakakin Majalisar Tarayya, shi ma ya fice ya koma APC.
Awai kuma ‘yan jam’iyyar ANPP wadanda suka fito aka yi gamin-gambiza da su.
Akwai irin su Nasir El-Rufai, wadanda adawa da Jonathan ta sa suka bi Buhari a cikin CPC, kuma suka yi kaka-gida a gaban Buhari, duk kuwa da cewa a baya lokacin sun a PDP, su ne suka hana Buhari yin nasara, kuma wadanda ke a sahun gabar nuna wa ‘yan Najeriya rashin dacewar Buhari ya zama shugaban kasa.
Akwai gwamnonin Arewa da wasu na kudu, irin su Rabi’u Kwankwaso, Wamakko, Rotimi Ameachi da sauran su.
Akwai irin su Rochas Okoroacha ‘yan jam’iyyar APGA, wanda gwamna ne. Akwai kuma irin su Aminu Bello masari, wadanda sun yi PDP, ACN, CPC, sannan suka dira cikin APC.
Sannan kuma akwai gaggan sanataocin da a baya sun taba yin gwamna har zango biyu, ko zango daya, wadanda ‘yan PDP ne, irin su Bukola Saraki, Danjuma Goje, Abdullahi Adamu, Kabiru Gaya.
Akwai kuma sauran daidaikun manya da kananan masu rike da mukamai daban-daban na siyasa.
BAYAN CIN ZABEN 2015
Bayan APC ta yi nasara a zaben 2015, bangaren Bola Tinubu, wato jam’iyyar ACN ta samu Mataimakin Shugaban Kasa. Yayin da CPC ta samu mukamin Shugaban Kasa. Yawancin Sanatoci kuma duk sun koma kujerar su, yayin da gwamnonin da suka fice daga PDP kuma wasu sun sake komawa, wasu sun zarce Majalisar Dattawa, kamar irin su Kwankwaso. Saura kuma suka tsaya jiran Buhari ya raba mukamai su samu na su rabon.
Bangaren Sabuwar PDP wadanda suka yi shadar-kuda suka fice daga PDP suka mara wa Buhari baya sai suka fahimci an raba manyan mukamai alhali su kuma ba su tashi da komai ba.
Da yake yawancin jiga-jigan su duk sun a cikin majalisar dattawa, sai suka fahimci cewa idan fa ba su tashi tsaye ba, to za a ci gari da yaki da su, sannan a bar su da cin ganimar kuturun bawa.
Hankalin su ya kara tashi sosai yayin da suka fahimci cewa uwar jam’iyyar APC ta fi so a bai wa Sanata Ahmed Lawal shugabancin Majalisar Dattawa.
SARAKI: KADANGAREN BAKIN TULUN APC
Ganin yadda shugabannin APC ke ta kartar kasa cewa sun fi so a bai wa Sanata Ahmed Lawal shugabancin Majalisa, sai Sanatocin da suka balle daga cikin PDP suka koma APC suka cewa APC na neman yi musu tsirara a kasuwa kenan.
Wannan ne ya sag aba dayan su suka mara wa Sanata Bukola Saraki baya, domini ya zama shugaban majalisar dattawa.
Sai dai kuma yawan su bai kai adadin wadanda dokar majalisa ta amince su yi nasara ga zaben ba. Hakan ne ya sa Saraki, wanda dama tun farko an ruwaito cewa ya janye shiga takarar shugabancin kasa tare da Buhari ne domin ya zama shugaban majalisar dattawa, ya mike tsaye neman yadda zai zama Shugaban Sanatocin ko ana ha-maza ha-mata.
Saraki da mabiya ko magoya bayan sa, sun rika yini su na kwananan kulla kisisina, kutunguila, annamimanci, kakuduba, kulle-kulle da kitimirmira, asarkala da kumbiya-kumbiyar yadda zai samu nasara.
Sun gano cewa za su iya hada kai da sanatocin bangaren PDP, amma hanya daya da hakan zai kai ga nasara, shi ne a bai wa PDP mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Saraki ya dauko Sanata Ike Ekweremadu na PDP, ya zama shi ne Mataimakin sa. Ya zama kadangaren bakin tulu kenan, a kashe shi a kashe tulu, a bar shi ya bata wuran da ke cikin tulun.
Wannan kuwa shi ne abin da masu iya magana ke cewa ‘ungulu da kan zabo’ kenan. Domin APC ce ta kafa gwamnati, Shugaban Majalisar Dattawa dan APC, amma mataimakin sa kuma dan jam’iyyar adawa, PDP.
Wannan abu ya tada hankalin jam’iyyar APC da sauran mukarraban gwamnatin Buhari, wadda a lokacin gwamnatin a cikin duhu ta ke tafiya ta na laube, domin ko ministoci ba a kai ga nadawa ba.
Ganin yadda Buhari ya yi sakacin da ya sa Saraki ya yi wa jam’iyyar APC da kuma gwamnatin sa wani sabon salo, wai kiran salla da goge, sai aka dauki karan tsana aka dora wa Saraki.
Jam’iyya da gwamnati ta rika yin baya-baya da shi, har ta kai ma ba a gayyatar sa wasu muhimman taruka.
Haka kuma ya kara janyo masa karan-tsana ga bangaren siyasar Bola Tinubu, da kae ganin shi ne jigon jam’iyyar APC.
RASHIN KARKON DANKON ZUMUNCIN APC
Tun tafiya ba ta yi nisa ba aka rika samun sabani da wasu jiga-jigan APC da ‘yan asalin Sabuwar PDP. Inda rigar rikicin ta ci gaba da barkewa, shi ne yadda aka rasa telan da zai dinke farkewar dinkin domin kada zaren dinkin jam’iyyar ya ci gaba da warwarewa.
Buhari a matsayin sa na Shugaban Kasa, ya sa-ido ya kyale jam’iyyar APC ta rika shiga cikin kazamin rikici a jihohin da ya ke da dimbin magoya baya, musamman a Kano da Kaduna da kewaye.
Kwankwaso ya samu sabani da Gwamna Ganduje, kamar yadda Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya rika gina wa kan sa katangar ta da raba shi da sauran ‘yan jam’iyya irin su Shehu Sani, Hakeem Baba Ahmed, Sanata Hunkuyi da wasu da dama.
Hakeem a Kaduna ya na daya daga cikin na hannun damar Buhari. Amma yadda El-Rufai ya yi kaka-gida bayan ya hau gwamna, hakan ta tilasta masa yin baya-baya da jam’iyyar, har aka yi masa bi-ta-da-kulli.
Duk irin rabon mukaman da Buhari ya rika yi, bai dora Hakeem a kan kowane mukami ba, duk da irin gudummawar da ya bai wa jam’iyyar APC.
Hasali ma Hakeeem ya koma shi ne Shugaban Ma’aikatan Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, wanda APC da gwamnatin Buhari ta dora wa karan-tsana.
ADAWAR GWAMNATIN BUHARI DA ‘YAN SABUWAR PDP
Jam’iyyar APC ta kara rincabewa, ta yadda yawancin mambobin Sabuwar PDP da ke cikin gwmnatin suka ko koma ‘yan adawar gwamnatin Buhari.
Abin mamakin kuma shi ne yadda ake bibiyar su da zargin laifukan da suka danganci kisa daya-bayan-daya.
A Kano, jami’an SSA sun cafke babban yaron Rabi’u Kwankwaso, mai suna Dangwani a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Kano, a kan hanyar sa ta zuwa Umra.
An tsare Dangwani, wanda ya yi wa Kwankwaso Shugaban Ma’aiktan Gidan Gwamnati a hannun SSS har tsawon kwanaki sama da 40, inda aka alakanta shi da zargin laifin da ke da nasaba da ta’addanci. An sako Dangwani kwanan nan a cikin watan Ramadan.
Har ila yau, a Kano, a fili ta ke cewa dimbin magoya bayan Kwankwaso ba za su zabi APC ba a zaben shugaban kasa, kuma za su yi wa Ganduje ‘anti-party.’
Ba su tsoro kuma ba su shakkar fitowa fili su na cewa su Kwankwasiyya suke yi, ba jam’iyya ba. Kuma duk inda Kwankwaso ya koma, bin shi za su yi, “ko jam’iyya ce mai daddawa da kuka.” Kamar yadda suke furtawa a cikin wakar Kwankwaso.
A Kaduna, jami’an ‘yan sanda sun aika wa Sanata Shehu Sani da takardar gayyata su na zargin sa da hannu a kisan kai.
Tuni a Kaduna Gwamna El-Rufai ya fito da dan takarar Sanata wanda su ke so zai maye gurbin Sanata Shehu Sani.
A jihar Kogi, an yi ta kadabolo da Sanata Dino Melaye, shi ma aka ce ya na da hannu a kisa da tashe-tashen hankula da harkallar bidigogi.
A jihar Kwara kuma an danganta Sanata Bukola Saraki da laifin fashi da makami.
Dukkan wadannan da alakanta da kisa, duk wadanda ba su dasawa da gwamnatin Buhari ne.
Wannan ya sa jama’a sun rika jefa waswasin cewa me ya sa idan ka na adawa da Buhari, sai a danganta ka da laifin aikata kisa?
KASHIN DANKAI A RABON MINISTOCIN BUHARI
Sabuwar PDP na jin haushin Gwamnatin Muhammadu Buhari sosai kamar yadda wasu ‘yan Arewa ke ji, ganin yadda aka dauki manyan mukamai masu romo da bargon tsotso aka dumbuza wa Shiyyar Kudu Maso Yamma, jihohin Yarbawa.
Jihar Kano, wadda ta fi bai wa Buhari yawan kuri’u, ta tashi da Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdur-Rahman Dambazau.
Jihar Zamfara ta samu babban mukami na ministan tsaro, sai dai kuma ba dan siyasa aka bai wa mukamin ba. Sannan kuma da yawa na ganin cewa bas u ga ranar sa a jihar Zamfara ba, domin duk da cewa dan jihar ne Ministan Tsaro, jihar sa ce aka fi karkashe talakawan ta kamar kisan feshin maganin kwari.
Baya ga Ministan Harkokin Kudade da Yankin Yarabawa ya samu, an ba yankin Ministan Lafiya, sannan kuma aka dauki manyan Ministoci uku duk aka damka wa tsohon gwamnan jiharf Lagos, Babatunde Fashola.
Fashola shi ne Ministan Makamashi, shi ne Ministan Ayyuka kuma shi ne Ministan Harkokin Gidaje.
Haka kuma Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida, mai suna Fowler, dan yankin ne.
Ministar Harkokin Kudade ta dakatar da Mannir Gwarzo daga aiki, wanda Shugaba Buhari ne ya nada shi. Haka shi ma Ministan Lafiya Adebowole ya dakatar da YHusuf, Shugaban Hukumar Inshorar Lafiyar Ma’aikata daga aiki, wanda shi ma Buhari ne ya nada shi.
Gwarzo dai ya shigar da kara a ranar Litinin da ta gabata ya na kalubalantar dakatarwar da Kemi Adeosun ta yi masa, domin ya ga gwamnatin da kuma jam’iyya ba ta damu da bibiyar dalilin da ya sa aka dakatar da shi ba.
APC DA SIRADIN 2019
Babban kalubalen APC shi ne zaben 2019 mai zuwa, wanda ga shi ya na tunkarowa amma kuma yam’iyyar sai kara shiga cikin rudani da rikice-rikice ta ke yi.
Sabuwar PDP da ke ganin ana yi musu rashin adalci da kuma bi-ta-da-kulli, sun ja na su layi daban, wanda a bisa dukkan alamu ko da an sake zama teburin sasantawa, an cimma wata jarjejeniya, to za a iya cewa dai ta-ciki-na-ciki.
Tambayar da ya kamata dan jam’iyyar APC ya yi wa kan sa ita ce, shin jam’iyyar karuwa ta ke yi daga 2015 zuwa yau, ko kuwa raguwa ta ke yi? Sai kuma tambaya ta biyu, idan Sabuwar PDP ta balle daga jikin APC, jam’iyya mai mulki za ta samu nakasa ko kuwa?
Su kuma ‘yan Sabuwar PDP, ga ta su tambayar: Za ku ci gaba a zaman mujiya a cikin tsuntsaye a jam’iyyar APC, ko ballewa za ku yi? Idan ku ka balle, ina za ku koma? A cikin PDP za ku yi ribas?
Hausawa dai sun ce ‘da-baya-da-baya ba ta gani.
Discussion about this post