Rashin albashi da ragwargwabewar cibiyoyin kiwon lafiya a jihar Filato ya saka mutanen jihar cikin halin kakanikayi

0

Mazaunan karamar hukumar Jos ta Yamma jihar Filato sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa cibiyoyin kiwon lafiya dake ke kauyukan jihar na gab da su zama kango.

Mutanen sun kara da cewa matsalolin da asibitocin gwamnati ke fama da su ya kai ga har gara su je asibitocin kudi maimakon na gwamnati duka da arhar sa.

” Babu yadda za a yi mu ci gaba da zuwa asibitin da suke karban haihuwa da fitillar kwai ga kuma rashin magungunan wai don na gwamnati ne.

Sanadiyyar wannan korafi da wadannan mazauna suka yi wakiliyar jaridar PREMIUM TIMES ta zazzagaya asibitocin yankin domin duba halin da wadannan asibitocin gwamnati ke ciki.

Da farko dai wakiliyar ta ziyarci asibitin Kerke dake karamar hukumar Jos ta yamma inda ta yi hira da ma’aikaciyar asibitin mai suna Grace Badung.

Grace wace ke kwance a kan tabarma tare da jaririyarta ta bayyana wa gidan jaridar cewa ma’aikatan asibitin sun dauke kafa daga zuwa aiki a asibitin gaba daya saboda rashin biyan su albashin su.

” Mukan hada watanni hudu kafin gwamnatin ta biya mu rabin albashin wata daya.”

Baya ga haka Grace ta ce suna fama da rashin bayan gida, rashin kayan aiki musamman magunguna, rashin wutan lantarki da rashin ruwa duk suna daga cikin matsalolin da ya kara korar ma’aikata da mutanen yankin zuwa asibitin.

A asibitin Rizek dake kauyen Zarazon kuwa wata ma’aikaciyar asibitin mai suna Ajiji Abigail ta bayyana cewa sai da suka yi tsawon watanni bakwai kafin gwamnati ta fara biyan su kashi 55 bisa 100 na albashin su duk da cewa suna biyan haraji kowani wata.

” Sannan rashin kayan aiki, wutan lantarki, ruwa, wurin zagawa da sauran su ya ya sa sauran ma’aikatan asibitin ba su zuwa aiki da ma marasa lafiya.

Wakiliyar ta kuma ziyarci asibitocin dake kananan hukumomin Bassa da Langtang, kamar wadanda suke kauyukan Fuskan Mata, Zalikali, Mista Ali, Layi, Kwampa da Pigani suma dai duk kanwar ja ce, matsalolin da wadancan ke fama da su shine suke fama da.

A karshe shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Miapkwap Livinus yace gwamnati ta kafa dokar da zai taimaka wurin dawo da kula da asibitocin a karkashin wannan gwamnati.

Ya ce hakan da gwamnatin ta yi zai taimaka wurin gyara wa da inganta cibiyoyin kiwon lafiya na jihar sannan ya kara da cewa gwamnati na aiki a asibitocin dake kananan hukumomin Bokkos da Mangu a yanzu haka.

Share.

game da Author