Kasar Koriya Ta Kudu ta yi wa Jamus mai rike da Kofin Duniya korar-kare zuwa gida, tun a wasan karshe na zagaye na daya, da ci 2-0.
Wannan ci da aka yi musu, ya maida Jamus na karshe a rukunin, tunda dama a wasan ta na farko, Mexico ta lallasa ta da ci daya mai ban-haushi. Sai dai ta yi nasara kan Sweden da ci 2-1.
Irin haka aka yi wa Faransa mai rike da kofi a gasar ci Kofin Duniya na 2002, inda aka yi waje-rod da ita tun a zagaye na farko, bayan ta ci kofin a gasar 1998.
Rabon da a fitar da Jamus a wasan zagaye na farko tun a 1938.
Kasar Italiya ta hadu da wannan tsautsayin a 2010, inda aka fitar da ita a zagayen farko, bayan da ta ci kofi a 2006. Spain ma ta hadu da wannan tsautsayin a 2014, bayan da ta yi nasarar lashe kofin a 2010.
Gasa uku kenan a jere ana cire mai rike da kofi a zagaye na farko.